Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a fadar Shugaban kasa don nuna murnarsa dangane da sake zabensa da aka yi a Ankara a Turkiyya ranar 28 ga watan Mayu shekarar 2023.
Yayin da yake jawabi ga kasar, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan bayan da kwarya-kwaryar sakamakon zaben 2023 ya fara shigowa ya ce nasararsa nasara ce ga dimokradiyya.
Lokacin da yake jawabi a gaban duban magoya bayansa wadanda suka taru a fadar shugaban kasa a Ankara, Shugaba Erdogan ya jaddada muhimmancin hadin kai, inda ya ce mutanen Turkiyya miliyan 85 da dimokuradiyya Turkiyya su ne suka yi nasara.
"Ba mu kadai ba ne muka yi nasara ba. Turkiyya ce ta yi nasara, dimokradiyyarmu ce ta yi nasara," in ji Erdogan.
"Babu wanda ya yi rashin nasara a yau. Duka mutane miliyan 85 sun yi nasara. Yanzu lokaci ne na hadin kai don samun cimma burin kasarmu da muradinta."
Shugaban Hukumar Koli ta Zaben Kasar (YSK) ya sanar da cewa Erdogan ne ya yi nasara a zaben a ranar Litinin da yamma.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Ankara, Shugaban Hukumar Zaben Ahmet Yener ya ce Erdogan ya samu galaba a kan dan takarar 'yan hamayya Kemal Kilicdaroglu a zagaye na biyu na zaben da aka gudanar.
Kamar yadda aka tattara alkaluman wadanda ba hukumance ba, Erdogan ya samu kaso 52.24 cikin 100 yayin da Kilicdaroglu ya samu kaso 47.86 cikin 100 na duka kuri'un da aka kada, ya ce, an kidaya kaso 99.43 na kuri'un da aka kada.
"A daya daga cikin manyan zabuka a tarihin siyasar jam'iyyu da dama a kasar nan, kasarmu ta zabi 'Shekaru 100 na Turkiyya'," in ji Erdogan.
Ya kuma cewa magoya bayansa cewa zaben "shi ne mafi muhimmanci" a tarihin Turkiyya na baya-bayan nan. "Ya kamata mu yi aiki ba dare, ba rana don al'ummarmu," Erdogan said.
Murmurewa daga girgizar kasar ranar 6 ga watan Fabrairu da kuma sake gina biranen da suka ruguje za su kasance manyan abubuwan da gwamnati za ta saka a gaba, in ji shi.
Erdogan ya ce kasar tana da karfi kuma za ta zauna a gurbin da ya dace da ita a tsakanin kasashen duniya.
Ya kuma tuna wa mutane cewa yau wato ranar 29 ga watan Mayu rana ce da ta yi daidai da ranar da Sarkin Daular Ottoman Mehmet II ya karbe iko da birnin Istanbul a shekarar 1453.
"Karbo Istanbul wanda muke bikin tunawa da shi a yau wato cika shekara 570 ke nan, hakan yana ishara da wani sabon babi yayin da kuma aka zo karshen wani tsohon babi," in ji Erdogan.
"Muna fatan kamar yadda wannan lokaci yake muhimmi ga tarihin Cika Shekara 100 da kafuwar Turkiyya kuma muna ganin wadannan zabuka a matsayin wata hanya ta tunawa da hakan."
Erdogan ya kuma soki kafafen yada labarai na Kasashen Yamma kan farfagandar da suke yadawa kan muradinsa na sake yin takara.
"Kafafen yada labaran Kasashen Yamma ba su yi nasara ba," in ji shi, ya ci gaba da cewa sun wallafa labarai "don su ga bayansa."
Game da batun komawar 'yan gudun hijirar Syria bisa radin kansu, Erdogan ya ce: "Zuwa yanzu mun taimakawa kimanin 'yan gudun hijirar Syria mutum 600,000 wadanda suka koma wasu bamgarori na Syria da ke da zaman lafiya.
"Ta hanyar wani sabon shirin tsugunar da 'yan gudun hijira da muke yi da hadin gwiwa da kasar Qatar, za mu tabbatar da fiye da miliyan data sun koma gida a shekaru masu zuwa."
Fiye da 'yan Syria miliyan uku da dubu 700 ne suke zaune a Turkiyya. Bayan fara yakin basasa a kasar Syria a shekarar 2011, Turkiyya ta "bude kofofinta" ga 'yan Syria wadanda suka guje wa tsangwama da cin zarafi.
Syria ta fada yakin basasa a farkon shekarar 2011, bayan da gwamnatin Bashar al Assad ta murkushe masu zanga-zanga goyon bayan tsarin dimokradiyya da karfin tuwo.
Dubbannin daruruwan mutane ne aka kashe kuma wasu miliyan 10 ne suka kauracewa muhallinsu, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.