"Turkiyya ta kai matsayin ƙasar da ta fi aikewa da agajin gaggawa zuwa Gaza a duniya da jimillar tan 50,000 na taimakon jinƙai da aka aike zuwa yanzu," in ji shi. /Hoto: AA

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa Turkiyya ce ke jagorantar ƙasashen duniya wajen taimakon da aka aikawa Gaza.

Ya zuwa yanzu, an aike da tan dubu 50 na agajin jinƙai zuwa yankin da aka yi wa ƙawanya inda ake ci gaba da kai farmakin Isra'ila, in ji Erdogan a ranar Litinin a wani taron da aka gudanar a Ankara babban birnin Turkiyya.

"Turkiyya ta kai matsayin ƙasar da ta fi aikewa da agajin gaggawa zuwa Gaza a duniya da jimillar tan 50,000 na taimakon jinƙai da aka aike zuwa yanzu," in ji shi.

Erdogan ya ƙara da cewa, Turkiyya, tare da gwamnatinta, da 'yan ƙasar, da ƙungiyoyi masu zaman kansu, sun yi fice a matsayin "ɗaya daga cikin al'ummomin" da suka "fi dacewa" su yi la'akari da ƙalubalen da suka shafi Gaza.

Mummunan yaƙin Isra'ila a Gaza

Isra'ila ta kai hari a Zirin Gaza na Falasdinu a matsayin ramuwar gayya kan harin wuce gona da iri da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban bara, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 1,200.

Kimanin Falasdinawa 34,700 ne sojojin Isra'ila suka kashe a Gaza tun daga lokacin da akasarinsu mata ne da kananan yara, yayin da wasu 78,000 suka jikkata, a cewar hukumomin lafiya na Falasdinu.

Kusan watanni bakwai da yakin Isra'ila, yankunan Gaza da dama sun lalace, lamarin da ya jefa kashi 85 cikin 100 na al'ummar yankin cikin ƙauracewa gidajensu sakamakon rashin abinci da ruwan sha da magunguna, a cewar MDD.

Ana tuhumar Isra'ila da laifin kisan kiyashi a Kotun Duniya. Hukuncin wucin gadi da aka yanke a watan Janairu ya ce, a fili yake cewa Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Gaza, sannan ta umarci Tel Aviv da ta dakatar da irin wannan aika-aikar tare da daukar matakan tabbatar da cewa ana ba da taimakon jin kai ga fararen hula a can.

TRT World