A ranar 26 ga Afrilu za a kaddamar da fara aikin TRT Saniyanci, sabon tsarin yada labarai ta shafukan sadarwa na zamani. / Hoto: TRT World

Kafar yada labarai ta Turkiyya, TRT, a karon farko za ta karɓi baƙuncin Babban Taron Kasashen da ke Magana da Yaren Sifaniyanci da ƙaddamar da kafar TRT Espanol (Sifaniyanci) a Istanbul a ranakun 25 da 26 ga Afrilu, da manufar haɓaka muryar ƙasar a duniya.

Babban Taron zai kuma gabatar da ƙaddamar da tashar TRT Espanol (Sashen Sifaniyanci na TRT), da zai fara gabatar da shirye-shirye a shafukan sada zumunta da shafukan intanet.

Mahalarta taron sun haɗa da Janaral Manaja 17 da 'yan jarida 21 da shugabannin zartarwa 16 daga ƙasashe 18 da ke magana da harshen Sifaniyanci irin su Sifaniya da Mexico da Colombia da Ajantina da Peru da Venezuela da Guatemala da Ecuador da Bolovia.

Bugu-da-ƙari, ɗaliban 40 daga Latin Amurka da Spaniya da ke karatu a Turkiyya za su halarci taron.

Taron zai fara da taron horarwa ga 'yan jaridu daga kasashen da ke magana da yaren Sifaniyanci a ranar 25 ga Afrilu.

Taken bayar da horon shi ne "Aikin Jarida na Kasa da Kasa", kuma zai mayar da hankali kan batutuwa irin su aikin jarida na gaskiya, abubuwan da jama'a suke tsammani, alakar kasa da kasa, da tasirin siyasa ga kafafen yada labarai, da kuma musayar ra'ayoyi.

Batutuwan muhawara a wajen taron

A ranar 26 ga Afrilu, za a kaddamar da sabuwar tashar ta yanar gizo, TRT Sifaniyanci.

Za a bude taron da fara gudanar da jawabin bude taro daga Daraktan Sadarwa na Fadar Shugaban Kasar Turkiyya Fahrettin Altun, da Darakta Janar na TRT Mehmet Zahid Sobaci.

Bayan ƙaddamar da TRT Sifaniyanci, da rana kuma za a gudanar da tarukan muhawara da tattaunawa tare da ƙwararrun mahalarta.

Batutuwan da za a tattauna a zaman muhawarorin sun hada da: "Karfafa Fahimtar Juna Ta Hanyar FIna-Finai Masu Dogon Zango: Turkiyya da Kasashen da ke magana da Yaren Spaniyanci," "Alakar Turkiyya da Kasashen da ke magana da Yaren Spaniyanci ta Fuskar Kafafan Yada Labarai: Manufar Bai-Daya da Kabulabale a Nan Gaba," da kuma "Sauyawar Samun Labarai a Duniya: Habaka Muryoyin Kasashe masu magana da Yaren Sifaniyanci don Fahimtar Duniya da Adalci."

Hade bangarorin al'adu

A karkashin taken "Wajen da Mutane ke da Daraja," TRT Sifaniyanci na da manufar hade bangarorin al'adu biyu waje guda ta hanyar gabatar da ingantattun labarai da wakiltar abubuwan da ke afkuwa a duniya da mahanga ta musamman.

Za ta bayar da labarai da shirye-shirye na musamman ga masu magana da yaren Spaniyanci, yaren da ake magana da shi a kasashe sama da 20 a duniya.

Haka zalika, za ta dinga kawo labaran da suka shafi jama'ar da ke magana da yaren Sifaniyanci, harshen da ake magana da shi a kasashe sama da 20 a duniya.

Sannan kuma, shafukan sada zumuntar zai tattara kusan mutane rabin biliyan a waje guda, yana haskaka mabambantan al'adu, fasaha da basira, da yalwa ta hanyar gabatar da labarai na musamman. Wannan babbar murya za ta yi amo daga Turkiyya zuwa Latin Amurka.

TRT Afrika