A Calgary, sararin samaniyar ya zama launin ruwan goro saboda yadda hayakin ke lullube garin / Hoto: AP

Kanada ta yi kira ga kasashen duniya da su taimaka mata wajen kashe mummunar gobarar dajin da aka kasa shawo kanta a fadin kusan rabin yankunan da ke yammacin kasar.

Gobarar, wacce ta yi mummunar barna a lardin Alberta mai arzikin man fetur a kwanakin baya-bayan nan ta yadu zuwa yankunan British Columbia da na Saskatchewan da ke makwabtaka da yankunan da wutar ke ci, da ma wasu yankunan na Arewacin kasar.

'Yan kwana-kwana 2,500 ne daga fadin Kanada wadanda jami'an soji ke taimaka musu ke kokarin kashe wutar a yankin Alberta, wacce tuni ta kona fiye da eka 500,000 na dazuka da gonaki, tare da lalata gidaje da kasuwanci da dama.

Amma jami'ai sun ce duk wannan kokari bai wadatar ba wajen kashe wutar.

"Halin da ake ciki a Alberta mai matukar muni ne," kamar yadda Ministan Kula da Kiyaye Al'umma Bill Blair ya shaida wa manema labarai a Ottawa ranar Laraba.

Blair ya ce Cibiyar Kashe Gobarar Daji ta Kanada "tana neman taimakon kasashen waje kamar su Amurka da Mexico da Australia da New Zealand... Muna rokon su zo su taimaka mana."

Hayakin gobarar dajin ya lullube yankin yammacin Kanada, lamarin da ya jawo aka yi gargadi kan illar da iskar da za a dinga shaka za ta yi ga lafiya.

A Calgary kuwa, sararin samaniyar ya zama launin ruwan goro saboda yadda hayakin ke lullube garin.

Daruruwan kilomita daga gabas kuwa, mazauna yankin Regina da Saskatoon a lardin Saskatchewan da ke makwabtaka sun ce sun wayi gari sararin samaniyar yankin ya turnuke da hayakin da warinsa da ya lullube ko ina.

'Bala'in da ba a taba gani ba'

Wurare 180 ne suke ci da wuta a fadin yankin - inda lamarin ya yi matukar munin da aka kasa shawo kansa a wurare 48 - abin da ya tursasa wa dubban mutane tserewa a mako biyun da suka gabata.

An dage umarnin hana kwashe mutane da aka sa a wasu yankunan a ranar Talata da Laraba, ciki har da Drayton Valley da yammacin Edmonton a Alberta da Fort St. John a British Columbia, saboda an samu damar dakile gobarar wuraren.

Kanada na fama da yawan gobarar daji a 'yan shekarun nan sakamakon mummunan yanayi da dumamar da duniya ke yi.

Hakan ya jawo ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa da gobarar daji da dama da suka yi sanadin cinye gari guda sukutum da tsananin zafin da ya hallaka fiye da mutum 500 a shekarar 2021.

TRT World