Game da TRT Afrika

Kafar labarai ta TRT Afrika, bangare ne na Gidan Rediyo da Talabijin na Türkiye (TRT) wato babbar tashar sadarwa ta kasar Türkiye.

An kafa shafin intanet na TRT Afrika a watan Maris na 2023, a wani bangare na manyan manufofin TRT na yada labarai ta intanet a cikin harsuna daban-daban, a yayin da duniya ke kara zama dunkulalliya a fagen sadarwa da yada labarai.

TRT Afrika na yada shirye-shirye da harsuna hudu; Ingilishi da Faransanci da Hausa da kuma Swahili.

Wadannan shafukan sun shiga sahun sauran shafukan intanet na TRT: TRT WORLD da TRT Français da TRT Arabi da TRT Balkan da TRT Russia da TRT Deutsch.

TRT Afrika na bai wa jama’a ingantattun labarai da sanar da su halin da duniya ke ciki da sanya musu karsashi da ba su damar bayyana ra’ayoyinsu, da kuma hanzarta bayar da labarai na hakika game da al’amuran da suka shafi rayuwarsu.

TRT Afrika na kuma bayar da labarai da rahotanni masu muhimmanci game da nahiyar wadanda ba a faye bayar da su ba.