Shugaba Mahamat Idris Deby yana takarar shugaban kasar Chadi a zaben da za a yi na g ga watan Mayu. Hoto: Reuters

Amurka za ta janye yawancin sojojinta daga Chadi da Nijar yayin da take ƙoƙarin maido da muhimman yarjejeniyoyin da suka shafi rawar da sojojinta za su taka wajen yaƙi da ta'addanci, in ji ma'aikatar tsaron Amurka a ranar Alhamis.

Dukkan ƙasashen Afirka biyu dai na da hannu a yunƙurin da sojojin Amurka ke yi na yaƙi da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a yankin Sahel, amma gwamnatin mulkin Nijar ta kawo ƙarshen wata yarjejeniya a watan da ya gabata, wacce ta bai wa sojojin Amurka damar gudanar da ayyukansu a ƙasar da ke yammacin Afirka.

A cikin 'yan kwanakin nan, maƙwabciyar Nijar ɗin wato Chadi ita ma ta nuna shakku kan ko yarjejeniyar da aka cim ma ta shafi sojojin Amurka da ke aiki a can.

Sakataren yaɗa labarai na Pentagon, Manjo Janar Pat Ryder, ya faɗa a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai cewa, Amurka za ta mayar da kusan dakaru 100 da ta girke a kasar Chadi.

Wani jami’in Amurka da ya nemi a sakaya sunansa ya ce wasu gomman dakaru na musamman da ke kasar Chadi a matsayin masu tsara tsare-tsare da masu ba da shawara za su koma Jamus a yanzu.

A farkon wannan watan ne babban hafsan sojin saman Chadi ya umarci Amurka da ta dakatar da ayyukan da ake yi a wani sansanin sojin sama da ke kusa da N'Djamena babban birnin ƙasar, kamar yadda wata wasiƙa da aka aike wa gwamnatin riƙon ƙwarya da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani.

A cikin wasiƙar mai ɗauke da kwanan wata 4 ga Afrilu Ministan Tsaron ƙasar Chadi, babban hafsan sojin sama Idriss Amine Ahmed ya ce ya shaida wa jami'an tsaron Amurka da su dakatar da ayyukan Amurka a sansanin jiragen sama na Adji Kossei bayan "Amurkawa" sun kasa samar da wasu takardu da ke tabbatar da kasancewarsu a can.

'Janyewa bisa oda'

“Yayin da ake ci gaba da tattaunawa da jami’an ƙasar Chadi, a halin yanzu AFRICOM na shirin mayar da wasu sojojin Amurka daga ƙasar Chadi, wadanda tuni aka shirya barin wasu sassansu. Wannan wani mataki ne na wucin-gadi a zaman wani ɓangare na ci gaba da nazari kan hadin gwiwarmu na tsaro, wanda zai ci gaba da kasancewa bayan zaɓen shugaban ƙasar Chadi a ranar 6 ga watan Mayu," in ji Ryder.

A jamhuriyar Nijar, yawancin ma'aikatan Amurka 1,000 da aka tura can su ma ana sa ran za su tashi, in ji Ryder.

Jami'an Amurka sun je Yamai ranar Alhamis domin fara tattaunawa kan janye sojojin Amurka cikin tsari da sanin ya kamata," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Laraba.

Ana sa ran taruka za su biyo baya tsakanin manyan jami'an Pentagon da Nijar a mako mai zuwa "don daidaita tsarin janyewar cikin gaskiya da mutunta juna," in ji Ryder.

TRT Afrika da abokan hulda