Ba a samu ''alƙalluma mai yawa ba suka yi nuni kan alamun cutar da ke cikin ruwan ba”/ Hoto: Reuters      

Mutane ƴan kalilan ne a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE suka nuna alamun wata cuta da ake zargin tana da alaƙa da gurɓataccen ruwa, bayan ruwan sama mai ƙarfin gaske da aka yi wanda ya haifar da ambaliya a makon jiya, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta kasar.

Sai dai a sanarwar da kamfanin dillancin labarai ta kasar ta fitar a ranar Laraba, ba ta bayyana takamaiman adadin mutanen da suka kamu da cutar ba, da kuma iri maganin da aka ba su.

''Ba a samu alƙaluma masu yawa ba kan mutanen da suka nuna alamun kamuwa da cutar wadda ke da alaƙa da gurɓataccen ruwa'', kuma suna samun kulawa daga asibiti, a cewar ma'aikatar.

Kana ba ta bayyana wacce irin cuta ce ta gurbata ruwan ba.

A ranar 16 ga watan Afrilu ne aka tafka ruwan sama mai ƙarfin gaske a ƙasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda ya haifar da tsaiko ga wasu sassan kasar ta yankin Gulf, lamarin da ya yi sanadiyar mamaye wasu birane da suka haɗa da Dubai da kuma yankunan arewacin kasar.

Mutane hudu sun mutu sanadin ambaliyar

Ma'aikata uku ƴan kasar Philippines sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Wasu mata biyu ne suka mutu a cikin motarsu yayin ambaliyar, sannan wani mutum da ya mutu a lokacin da motarsa ta fada cikin wani rami, kamar yadda ma'aikatar kula da baƙi ta Philippines ta sanar.

Jimillar mutanen da suka mutu sun kai hudu idan aka hada da wani dattijo mai shekara 70 da ruwan ya tafi da shi a cikin motarsa a Ras Al-Khaimah, daya daga cikin masarautun yankin Gulf guda bakwai mai arzikin man fetur.

TRT World