Ambaliyar ruwa: Yadda ake binne mutanen da suka mutu a Libya

Ambaliyar ruwa: Yadda ake binne mutanen da suka mutu a Libya

Hukumomi a Libya sun ce mutanen da suka mutu a birnin Derna na kasar sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta fada wa kasar za su iya kai wa tsakanin 18,000 zuwa 20,000. Magajin birnin Abdulmenam al Ghaithi ne ya bayyana haka ranar Laraba da maraice. Ya yi bayanin ne a yayin da ake ci gaba da binne mutanen da suka mutu sannan dubbai suka bata sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a kasar ranar Lahadi.