Wata tawagar masu shiga tsakani daga Masar za ta je Isra'ila a wani mataki da manema labarai suka ce sabon yunkuri ne na neman tsagaita wuta. / Hoto: AA

1241 GMT — Zanga-zangar goyon bayan Gaza alama ce ta ƙarfin dimokradiyya: Blinken

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce zanga-zangar da ake yi a jami’o’in Amurka kan adawa da yaƙin da ƙawar Amurkar Isra’ila ke yi a Gaza alama ce ta ƙarfin dimokraɗiyyar Amurka, sai dai ya soki abin da ya kira “shirun” da ake yi a kan ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas.

"A kasarmu, alama ce ta dimokuradiyyarmu, 'yan kasarmu suna bayyana ra'ayoyinsu da damuwarsu da fushinsu a kowane lokaci, kuma ina ganin hakan yana nuna karfin kasar da karfin dimokuradiyya," in ji Blinken. .

1257 GMT — Netanyahu ya zama 'mahaucin da ke kisa a Gaza' — Erdogan

Firaiministan Isra'ila ya sanya sunansa a cikin tarihi inda ya zama mahaucin da ke kisa a Gaza, a cewar shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Da yake jawabi a Istanbul, ya ce duk wanda yake "son ganin fir'auna a wannan zamanin, ya kalli mutumin da ya yi kisan rashin imani na Falasdinawa fiye da 35,000 a cikin kwana 203".

Ya ƙara da cewa Turkiyya za ta ci gaba da fafutukar ganin Falasɗinawa sun samu ƴanci, yana mai cewa kada kowa ya yi tunanin cewa mahukuntan Ankara za su yi gum da bakinsu a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kisan ƙare-dangi a Gaza.

1150 GMT — Amurka ta ce ta lalata jiragen yaƙi marasa matuƙa na Houthi bayan harba makami mai linzami a Yemen

Rundunar sojin Amurka ta ce dakarun ƙawance sunlalata jiragen yaƙi guda biyu marasa matuka a yankunan da ‘yan Houthi ke iko da su a Yemen bayan da ‘yan tawayen da ke samun goyon bayan Iran suka harba makami mai linzami a Mashigin Tekun Aden.

Makami mai linzamin da aka harba a ranar Alhamis bai haifar da wani rauni ko barna ba, in ji Babban Kwamandan Amurka (CENTCOM), a cikin wata sanarwa ta X.

Awanni bayan hakan ne rundunar sojin Amurka ta yi nasarar lalata jiragen a yankunan da Houthi ke iko da su.

0825 GMT — Dakarun Isra'ila sun kama Falasɗinawa 7 a samamen da suka kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Kamfanin dillancin labaran Falasɗinu (Wafa) ya ruwaito cewa dakarun Isra'ila sun kama Falasɗinawa bakwai, cikinsu har da wata mace, a samamen da suka kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan ranar Juma'a da sanyin safiya.

A yankin Ramallah, wasu sojojin Isra'ila sun kai samame a sansanin ƴan gudun hijira na Al-Jalazon, inda suka tsare Falasɗinawa uku, ciki har da wata mace mai shekara 33 mai suna Jehad Nakhla.

A lardin Jenin, dakarun Isra'ila sun shiga garin Qabatiya sannan suka kama Falasɗinawa biyu bayan sun yi bincike a cikin gidansu.

Wasu sojojin Isra'ila sun kai samame a sansanin ƴan gudun hijira na Balata da ke arewacin birnin Nablus da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, inda suka tsare wani Bafalasɗine.

Dakarun Isra'ila sun gudanar da samamen ne da daddare har zuwa safiya./Hoto:AA

2330 GMT — Ana zargin Isra'ila da sace ɓsassan jiki daga gawawwakin da aka gano a kabarin bai-ɗaya a Gaza

Kamfanin dillancin labarai na WAFA ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatan jinya da masu aikin ceto sun tayar da shakku kan satar sassan jikin da sojojin Isra'ila ke yi bayan gano gawarwakin fararen hula daga kaburburan bai-ɗaya.

Likitoci da masu ceto sun gano akalla gawarwakin muumm 392 a Asibitin Nasser da ke Khan Younis. Kimanin 165 daga cikinsu har yanzu ba a san ko su waye ba bayan an gano gawarwakinsu sun lalace inda aka cire wasu sassan jikinsu.

Likitoci sun bayyana cewa an samu wasu gawarwaki tare da yanke cikinsu da dinke su ta wani salo da ya sha bamban da dabarun rufe raunuka da aka saba yi a Gaza, lamarin da ya sanya ake zargin satar gaɓoɓi, yayin da aka ga gawar wata ƙaramar yarinya sanye da rigar tiyata an cire wasu sassan jikinta, lamarin da ke nuni da cewa an binne ta tun tana raye.

Rahoton ya ce, an gano gawarwakin mutane da dama a lullube da baƙƙe da shuɗayen ledoji - irin waɗanda ake amfani da su wajen ƙara yawan zafin jiki - da suka sha bamban da launin likkafanin da ake amfani da su a Gaza, lamarin da kuma ke nuni da cewa Isra'ila na son hanzarta ɓoye hujjoji.

Ana zargin Isra'ila da sace ɓsassan jiki daga gawawwakin da aka gano a kabarin bai-ɗaya a Gaza / Photo: AA
TRT Afrika da abokan hulda