Amfani da E-Sukuta don kauce wa cunkoson Legas

Amfani da E-Sukuta don kauce wa cunkoson Legas

Wani matashi ya kafa kamfanin E-sukuta mai amfani da lantarki da zummar taimaka wa dalibai isa makarantunsu da wurwuri ba tare da fuskantar cunkuson ababen hawa na birnin Legas da ke kudancin Nijeriya ba. Isaac Oyedokun ya shaida wa TRT Afrika cewa matakin nasa yana rage gurbatar muhalli da ke faruwa sakamakon amfani da ababen hawa masu aiki da fetur.