Mai zayyana da ke farfado da rubutun Larabci a Nijeriya
Yushaa Abdallah fitaccen mai zayyana ne dan Nijeriya da ya yi karatu a Turkiyya. Ya kware a fannin zayyana ta Larabci da harshen Farisa. Yanzu ya mayar da hankali wurin koyar da matasa zayyana.