Ministan Ciniki da Masana’antu na Jamhuriyar Nijar, Abdoulaye Seydou, ya rattaba hannu kan wata doka da ta haramta fitar da man fetur da man gas daga ƙasar zuwa ƙasashen waje.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar, ANP, ya ruwaito cewa gwamnatin Nijar ta ɗauki wannan matakin ne domin aiki da wata doka da ta buƙaci wadata ƙasar da makamashi (man fetur da gas) kafin a sayar wa ƙasashen duniya.
Dokar ta ce idan aka samu rara ta man gas da man fetur, matatar man Nijar SORAZ da kamfanin man ƙasar SONIDEP za su iya fitar da rarar ne kawai bayan sun samu izini na musamman daga ministan da ke kula da cinikayya na ƙasar.
Kazalika dokar ta bayar da umarni ga ma’aikatan ma’aikatar kasuwanci da masana’antu da jami’an kwastam da dakarun tsaro tabbatar da wannan doka.
Wannan matakin na zuwa a daidai lokacin da ake fama da rashin mai a gidajen man babban birbin ƙasar Yamai, in ji ANP.
Rahotanni sun nuna cewa ƙarancin man yana shafar wasu birane ma na ƙasar.
Nijar ƙasa ce mai arzikin mai, kuma matatar SORAZ tana tace mai a cikin ƙasar.
Sai dai kuma abin da ake tacewa a cikin ƙasar a halin yanzu bai kai buƙatar ƙasar ba.
Ko a watan Agustan wannan shekarar, ƙasar ta sanya hannu kan wata yarjejeniya ta gina sabuwar matata mai iya tace gangan ɗanyen mai 100,000 a yini da wani kamfanin ƙetare.




















