Yadda ƙarin kuɗaɗen tallafi ke taimaka wa mata ‘yanwasan ƙwallon ƙafa da ke fama da nakasa a Kenya
Wata gidauniya da ke samun tallafi daga wani matashi, ta taimaka wa mata masu nakasa 'yanwasan ƙwallon ƙafa a Nairobi samun damar yin atisaye cikin aminci tare da dakile ƙalubalen da ke hana su cim ma burinsu a baya.

