| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 minti karatu
Turkiyya da Nijeriya sun ba da shawarar amfani da tsarin kudi na Musulunci a tattalin arzikin duniya
Jami’an Turkiyya da Nijeriya sun bayyana tsarin kuɗi a Musulunci a matsayin wata hanya ta taimakawa tattalin arzikin duniya jure matsalolin rashin tabbas, yayin taron koli na biyar na AlBaraka da aka gudanar a Landan.

Turkiyya da Nijeriya sun ba da shawarar amfani da tsarin kuɗi a Musulunci wajen magance sauye-sauyen tattalin arzikin duniya.

Jami’an Turkiyya da Nijeriya sun bayyana tsarin kuɗi a Musulunci a matsayin wata hanya ta taimakawa tattalin arzikin duniya jure matsalolin rashin tabbas, yayin taron koli na biyar na AlBaraka da aka gudanar a Landan.

Shugaban Hukumar Asusun Arzikin Turkiyya (TWF), Salim Arda Ermut, ya ce gogewar da ƙasar ta samu wajen tunkarar matsalolin siyasa da tsaro tsawon ƙarnuka na iya taimaka wa duniya wajen shawo kan ƙalubalen tattalin arziki na yanzu.

Ya bayyana cewa kuɗaɗen Musulunci, waɗanda suka ginu bisa rashin ruwa da ƙa’idojin ɗabi’a, na iya taimaka wa samar da ayyukan yi da bunƙasa kasuwanci da tattalin arziki.

A nata ɓangaren, Ministar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Nijeriya, Doris Uzoka-Anite, ta ce tsarin kuɗaɗen da aka tsara bisa ƙa’idojin Musulunci na iya biyan buƙatun tattalin arzikin duniya baki ɗaya, ba Musulmi kaɗai ba.

Ta kuma bayyana cewa tsarin bayar da Sukuk a Nijeriya ya taimaka wajen samar da kuɗaɗen gudanar da manyan ayyukan more rayuwar jama’a.

Taron ya haɗa ƙwararru da shugabannin harkokin kuɗi daga sassa daban-daban na duniya domin tattauna ɗabi’un kuɗi, sauye-sauyen fasahar zamani da sabbin damarmakin bunƙasa tattalin arzikin Musulunci.