Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana shirinsa na zuba jarin fiye da dala biliyan 10 a fannin wutar lantarki don shawo kan matsalar makamashi a Nijeriya da kuma bunƙasa masana’antu a shekaru uku zuwa huɗu masu zuwa.
Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kafar watsa labarai ta Al Jazeera, inda ya yi nuni kan rashin tabbas a manufofin gwamnati da kuma rashin isasshiyar wutar lantarki a matsayin manyan ƙalubale da ke hana 'yan Afirka saka hannun-jari a nahiyar.
Ya bayyana cewa yana duba yiwuwar karkata jarin kamfani ɗaya ko biyu na Dangote, ciki har da na ƙarafa zuwa ga fannin samar da wutar lantarki da haɓaka masana'antun wutar lantarki a faɗin nahiyar.
"Ina shaida muku, a cikin shekaru uku zuwa huɗu masu zuwa, za a samu babban sauyi a Afirka, shi ya sa muke duba wutar lantarki. Za mu saka hannun-jari a wutar lantarki. Akwai kasuwanci na kamfani ɗaya ko biyu da za mu iya sokewa, kamar na ƙarafa, za mu sanya kuɗin a ɓangaren wutar lantarki. Muna son zuba jarin fiye da dala biliyan 10 a ɓangaren wutar lantarki."
Dangote ya bayyana damuwa kan yadda ‘yan Afirka mutum fiye da miliyan 600 da ke ci gaba da rayuwa babu wutar lantarki, yana mai cewa dole ne nahiyar ta magance lamarin.
"Bai kamata mu 'yan Afirka mu bari mutum miliyan 600 daga cikin mutanenmu su ci gaba da zama cikin duhu ba," in ji Dangote.
Hamshaƙin attajirin ya danganta samar da wutar lantarki da ci-gaban tattalin arziki sannan ya jaddada cewa gwamnatocin da suka yi nasarar wajen samar da wutar lantarki ga 'yan ƙasarsu ba za su sha wahala wajen sake neman yaƙin neman zaɓe ba.
"Idan wasu 'yan siyasa suka yi aiki tuƙuru tare da tsari, ldan suka samar da wutar lantarki, to ba za su buƙaci zuwa yaƙin neman zaɓe a lokacin zaɓe ba. Wutar lantarki ita ce mabuɗin; ba za mu taɓa ƙirƙira ko samun ci-gaba ba tare da wutar lantarki ba. Shi ya sa suke cewa wutar lantarki ita ce ci-gaba. Idan na ce wutar lantarki, ina nufin wutar lantarki ita ce ci-gaba," in ji Dangote.
Ya ƙara da cewa "samun tsayayyiyar wutar lantarki mai inganci na da matuƙar mahimmanci wajen ƙirƙirar ayyukan yi da gina masana'antu masu ɗorewa," yana mai cewa dole ne 'yan Afirka su jagoranci saka hannun-jari a nahiyar don jawo hankalin masu zuba jari na ƙasashen waje.
Baya ga ɓangaren wutar lantarki, Dangote ya ce kamfaninsa zai faɗaɗa kasuwanci a fannin takin zamani domin zama babban mai samar da takin Urea a duniya nan da shekarar 2028.


















