Erdogan ya ce Turkiyya ta tsaya a matsayin kasa daya tilo da ke aiwatar da takunkumin hana fitar da kayayyaki zuwa Isra'ila a cikin rukunin kayayyaki 54. / Hoto: AA

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana a wani jawabi da ya yi a birnin Istanbul ga kungiyar 'yan majalisar Quds cewa, "Masallacin Ƙudus na birnin Ƙudus yana ƙara fuskantar tsangwama, tare da goge asalin tsohon birnin da Isra'ila ta yi (Urushalima).

Kamar yadda kare Ƙudus yake nufin kare bil'adama, zaman lafiya, da mutunta addinai daban-daban, Turkiyya za ta ci gaba da wannan gwagwarmaya da azama, in ji Erdogan a yau Juma'a ga wata kungiyar da ta sadaukar da kanta wajen kare birnin.

“Kakannina sun yi wa Birnin Ƙudus hidima shekara 400; Ba za a iya goge abin da suka yi ba,” in ji Erdogan, yayin da yake tuno da zamanin Daular Usmaniyya.

Ya kara da cewa duk wanda ke neman "Fir'aunawan zamani bai kamata ya yi nisa ba, ya dubi wadanda suka kashe Falasdinawa 35,000 ba tare da tausayi ba a cikin kwanaki 203 da suka wuce," yana mai nuni da hare-haren da Isra'ila ta dauki tsawon watanni tana kai wa Gaza.

"Netanyahu, kamar miyagun da suka gabace shi, ya sanya sunansa a tarihin abin kunya a matsayinsa na mahaucin Gaza," in ji Erdogan.

A yayin da Falasdinawa a Gaza suka kwashe kwanaki 203 suna adawa duk da rashin jituwa, "babu wanda zai yi tsammanin za mu yi shuru wajen fuskantar kisan kare dangi," in ji shi.

"Za mu ci gaba da ganin 'yan'uwanmu na Hamas, wadanda ke kare kasarsu daga 'yan mamaya, a matsayin ƴan gwagwarmayar Falasɗinu," in ji shugaban.

Erdogan ya ƙara da cewa, Turkiyya ta tsaya a matsayin kasa daya tilo da ke aiwatar da takunkumin hana fitar da kayayyaki zuwa Isra'ila a cikin rukunin kayayyaki 54.

Ya ƙara da cewa, Turkiyya ita ma tana kan gaba wajen bayar da agaji ga Gaza, domin tun a ranar 7 ga watan Oktoba, Ankara ta aika da kusan tan dubu 50 na agajin jinƙai ta jiragen sama 13 da jiragen ruwa tara.

Ya kuma ce "tallafin soja da diflomasiyya da Amurka ke ba Isra'ila ba tare da wani sharadi ba, ba ya taimakawa wajen warware matsalar, sai dai yana ƙara ta'azzara matsalar."

Erdogan ya ƙara da cewa, yayin da aka kashe mutum 35,000 a Gaza ba tare da jinƙai ba, amincewa da shirin taimakon dala biliyan 25 ga Isra'ila da Majalisar Dattawan Amurka ta yi, shi ne abu mafi muni ƙarara a kan hakan.

Idan ana batun Isra’ila, “A kan manta da muradun Ƙasashen Yamma da suka hada da ‘yanci,da dimokuradiyya da bin doka da oda da ‘yancin fadin albarkacin baki da tunani, da kuma ‘yan jarida, an yi wasti gefe da su,” in ji shi.

Shugaban na Turkiyya ya kuma yaba da taron Majalisar Dokokin Birnin Ƙudus a matsayin murya da numfashin Falasɗinu.

TRT World