Alkaluman talauci da zamantakewar iyali a Nijeriya

Alkaluman talauci da zamantakewar iyali a Nijeriya

Shin kun san matan yankin da aka fi yi wa kishiya a Nijeriya? Sannan matan wanne yanki ne a Nijeriya suka fi cin zarafin mazajensu? Haka kuma matan wanne yanki ne suka fi mallakar filaye da gidaje a kasar? Wadannan na daga cikin batutuwan da suke ƙunshe a cikin binciken da wata cibiya mai bincike kan al’amuran da suka shafi hada-hadar kudade da rayuwar jama’a a Nijeriya ta fitar kan talauci da sha’anin zamantakewar iyali a kasar. A wannan bidiyon, Halima Umar Saleh ta fayyace mana alkaluman na cibiyar Statisense da ke Legas.