Ɗan Agajin da ya tsinci miliyoyin kuɗi ya mayar
Ɗan agajin nan da ya tsinci miliyoyin kuɗi ya kuma yi cigiyarsu, Salisu Abdulhadi, ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa ya shafe wata guda yana cikin fargaba a lokacin da ake ci gaba da cigiyar mai kuɗin a masallatai.
Ya ce bai samu kwanciyar hankali ba har sai da aka ce an samu mai kuɗin, kuma aka tabbatar da cewa ko kwabo bai yi ciwon kai ba.