Asalin tashe a ƙasar Hausa
Duk da sauyawar zamani da ci gaban da ake samu, har yanzu al’adar tashe ba ta gushe ba gaba daya a ƙasar Hausa.
Al’ada ce da mata da maza da yara da manya kan yi daga goma ta tsakiya ta watan azumi da rana ko da daddare, domin a dauke wahalar azumi ko a samu kudin shiga sannan a samu nishadi, kamar yadda masana harkokin al’adu suka shaida wa TRT Afrika Hausa a wannan bidiyon.