Hira ta musamman da Rahama Sadau

Hira ta musamman da Rahama Sadau

Rahama Sadau, fitacciyar tauraruwar fina-finan Nijeriya ta ce ba da gangan take yawan jawo ce-ce-ku-ce ba.A hira ta musamman da TRT Afrika Hausa, Rahama ta yi mana bayani kan abin da ya kawo ta Istanbul da rawar da take takawa a fina-finan Kannywood, Nollywood, Bollywood da kuma Hollywood.Kazalika ta yi mana karin haske kan batun aurenta, da dangantakarta da matan Kannywood da tasirin da Ali Nuhu ya yi a rayuwarta.Rahama Sadau ta yi tsokaci kan abin da ya sa take kaunar tauraruwar Bollywood Priyanka Chopra da kuma yadda take gudanar da mu’amala a cikin gidansu da kuma Idan  ta fito waje.