15 Disamba 2023

05:46

05:46
Ƙarin Bidiyoyi
Mace mai tuka tirela daga Nijeriya zuwa Nijar
Hauwa, mai shekara 26, direbar babbar mota ce da ta fara tuki tana da shekara 17 a duniya.
Ta ce ta fara sha'awar sana'ar tuki daga wajen 'yan uwanta wadanda suma direbobi ne. "Sai nake ji ina sha’awar aikin da maza ke yi,” in ji ta.
Direbar tirelar ta ce albarkacin sana’arta ta gina gida, tana da filaye biyu kuma ta dauki nauyin karatun kaninta. Hauwa ta fuskanci kalubale iri-iri kuma ta yi kira ga mata kan muhimmancin sana’a da kuma dogaro da kai.
Ƙarin Bidiyoyi