Ziyara Zuwa Masallacin Hagia Sophia
Katafaren Masallacin Hagia Sophia da ke birnin Istanbul na Turkiyya ya kasance wani waje da ke jan hanaklin masu yawon bude ido daga fadin duniya.
A da wajen coci ne a lokacin Daular Rumawa tsawon kusan shekara 1,000, sai kuma ya koma masallacin a zamanin Daular Usmaniyya har tsawon shekara kusan 500, sai kuma ya koma wajen adana kayan tarihi tsawon shekara 85, sannan a shekarar 2020 aka sake mayar da shi masallaci.
A wannan bidiyon, za ku ga bayanai masu muhimmanci a kansa a ziyarar da TRT Afrika ta kai.