Andre Onana, tsohon golan Manchester United ya ce bai taɓa ganin soyayyar da ya gani a ƙungiyar Trabzonspor ta Turkiyya ba, inda ya koma aro a makon nan.
Onana ya kammala komawa Trabzonspor aro bayan da aka tilasta masa barin Man U, inda aka rage masa daraja a zaɓar masu buga wasa ƙarƙashin koci Ruben Amorim.
Ɗan asalin Kamaru, Onana ya je United ne a 2023 kan kuɗi fam miliyan 47.2.
A yanzu zai nemi farfaɗo da tagomashinsa a gasar Super Lig ta Turkiyya, inda ya bayyana tsananin farin cikinsa da yadda ya samu tarba a Turkiyya.
A maraicen Alhamis ne Manchester United ta tabbatar da ƙaurar Onana mai shekaru 29 zuwa Trabzonspor a matsayin aro na tsawon kakar 2025-26.
Kocin United ya zaɓi yin aiki tare da golansa na biyu Altay Bayindir, kafin daga bisani ya sayo wani golan, Lammens kan fam miliyan 18.2.
Kurarin Onana
Da yake jawabi ga manema labaran Turkiyya yayin da ya sauka a ƙasar don sanya hannu kan kwantiragi, Andre Onana ya ce “Ina murna matuƙa, zan fara sabon babi da sabuwar rayuwa”.
“Ban taɓa ganin irin soyayya haka ba daga mutanen da suka kewaye ni. Abin alfahari ne da aka sanya ni jin tamkar a gida nake tun a wunin farko na zuwana nan.”
"Ina fatan fara aiki ba ɓata lokaci don rama soyayyar da aka nuna min ta hanyar faranta rayuka a filin wasa. A shirye nake a koyaushe."
A yanzu dai Onana ya rufe babin da ya yi fama da rashin tabbas a ƙoƙarinsa, inda ya yi ƙaurin suna wajen tafka kurakurai a Old Trafford.
Sannan zai yi ƙoƙarin ganin ya samu gurbi a tawagar ƙasarsa ta Kamaru da ke da damar samun cancantar buga gasar Kofin Duniya na 2026.
Sabuwar ƙungiyar tasa ta Trabzonspor tana mataki na biyu a teburin babbar gasar Turkiyya ta Super Lig.
Ranar Lahadi mai zuwa za su kara da Fenerbahce, inda Onana zai yi fatan fara buga wasa bayan an tabbatar masa da cewa zai saka jesi mai lamba 24.