A jerin tawagar da za ta fara buga Gasar Zakarun Turai ta kakar 2025-26, Real Madrid ta saka sunan tauraron ɗan wasanta Jude Bellingham, wanda ya je hutun jinyar watanni.
A Talatar makon nan ne Madrid za ta kara da Marseille ta Faransa, inda a yanzu ta tabbata cewa ɗan wasan nata da ya warke daga tiyata a kafaɗa zai taka mata leda.
Ana kallon dawowar Bellingham a matsayin wani babban ƙaimi ga ƙungiyar, wanda kuma yake nuni da warakar ɗan wasan ɗan asalin Ingila.
Rabon da ɗan wasan mai shekaru 22 ya buga wa Madrid wasa tun a Gasar Kofin Duniya na Ƙungiyoyi da ya gudana a Amurka a Yulin 2025.
Kafin yanzu, an yi tsammanin Jude Bellingham ba zai dawo ba sai watan gobe.
Shirin El Clasico
Bellingham dai ya samu gocewar ƙashin kafaɗarsa ta hagu ne a Nuwamban 2023 a wani wasan Gasar La Liga da Real Madrid ta buga da Rayo Vallecano.
A Yulin 2025, ciwon nasa ya taso inda aka masa tiyata a London, kuma aka ba shi makonni 10 zuwa 12 na hutun jinya.
A farkon watan nan na Satumba, kocin Real Madrid Xabi Alonso ya bayyana kyakkyawan fatan farfaɗowar Bellingham, wanda aka ruwaito cewa a lokacin ya fara yin atisaye.
A yanzu dai masoya Madrid za su yi fatan ɗan wasan zai warke garau don buga musu babban wasan kece rainin na El Clasico tare da Barcelona a Oktoba mai zuwa.