| Hausa
‘Ana yawan tambayata addinin da nake yi’
08:27
Duniya
‘Ana yawan tambayata addinin da nake yi’
Tauraro a shirin Kwana Casa’in mai dogon zango, John Dan Daso, ya ce mutane suna yawan tambayarsa kan ko shi Musulmi ne ko Kirista. Ya bayyana haka ne a hira ta musamman da TRT Afrika Hausa a birnin Kano na Nijeriya. John Dan Daso, wanda sunansa na ainihi shi ne Waziri Alhaji Salihu Hong, ya ce “Musulmi ne ni gaba da baya. Ina Sallah yadda Musulmai suke yi.” Ya kara da cewa rawar da yake takawa a matsayin Kirista a Kwana Casa’in ta nuna cewa ya gwanance wajen yin aikinsa tun da har wasu suke yi masa kallo a matsayin wanda ba Musulmi ba. Ya yi kira ga masu kallonsu da su rika yi wa ‘yan fim uzuri bisa wasu kura-kurai da suke aikatawa, yana mai cewa kowa yana iya yin kuskure.
11 Fabrairu 2024
Ƙarin Bidiyoyi
Nasiru-Deen na Ghana: daga dalibi zuwa jakada a Turkiyya
Kasarmu Nijar ita ce sama da komai: Janar Tiani
Kantin Kwari: Kasuwar tufafi mafi girma a Yammacin Afirka
Boko Haram: Halin da ‘yan gudun hijirar Nijeriya suke ciki a ƙasar Chadi
Lugude: Mutumin da ke wallafa tsofaffin hotunan arewacin Nijeriya
Zan iya auren mace irin Samira ta shirin Garwashi
Ba na so na samu matsala a Kannywood har lokacin da zan yi aure - Ma'u ta Fim ɗin Garwashi
Ni ‘yar Nijar ce amma ina alfahari da Nijeriya – Fati Nijar
Daɗaɗɗiyar kasuwar kwaɗi a Arewacin Nijeriya
Hanyar Abuja-Kaduna: Lalacewar hanya mafi muhimmanci a arewacin Nijeriya