Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Chadi Mahamat Deby. /Hoto: AFP

An rantsar da Janar Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban farar-hula na Chadi bayan ya jagoranci gwamnatin mulkin sojin Chadi tsawon shekaru uku.

A hukumance, Deby ya lashe zaɓe da kashi 61 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa ranar 6 ga watan Mayu, sai dai ƙungiyoyin ƙasashen duniya masu zaman kansu sun ƙalubalanci sahihancin zaɓen, sannan babban mai hamayya da shi ya ce an "tafka maguɗi".

A watan Afrilun 2021 wasu manyan Janar-Janar na sojoji 15 suka ayyana Deby a matsayin shugaban riƙon ƙwarya bayan mahaifinsa Shugaba Idriss Deby Itno, ya wanda ya shafe shekaru 30 yana mulki, mutu a fagen-daga a fafatawar da suka yi da 'yan tawaye.

Rantsar da Muhamat Deby ta kawo ƙarshen mulkin shekaru uku na soji a ƙasar wadda ke da matukar muhimmaci wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a yankin Sahel.

Goyon bayan ƙasashen duniya

A 2021 ne Deby ya samu goyon bayan kasashen duniya karkashin jagorancin Faransa wanda gwamnatocin mulkin sojin ƙasashen da ta yi wa mulkin mallaka wato Mali da Burkina Faso da Niger suka fattatki dakarunta daga ƙasashensu.

Bikin rantsarwar ya kuma gamu da sukar 'yan adawa, suna masu bayyana shi a matsayin mulkin gado na gidan Deby.

Succes Masra, daya daga cikin masu adawa da Deby tun kafin ya zama Firaminista, ya yi muraɓus daga muƙaminsa a ranar Laraba, sakamakon shan kaye da jam'iyyarsa ta yi a zaɓen bayan watanni hudu kacal da ya yi a kan karagar mulki.

Masra, masanin tattalin arziki da ya samu kashi 18.5 na kuri'un da aka kada, ya ƙalubalanci sakamakon zaben.

Hukuncin kotu

Mahamat ya samu nasara ne a zagayen farko na zaɓen sai dai ‘yan adawa sun zarge shi da tafka maguɗi da kama-karya..

Bayan majalisar tsarin mulkin Chadi ta yi watsi da yunƙurin Masra na soke sakamakon zaɓen, ya bayyana cewa a yanzu ''babu wata hanyar shari'a da ta dace'' kana ya yi kira ga magoya bayansa da su ci gaba da yin ''gangamin lumana".

Kawun Deby, Yaya Dillo Djerou, wanda ya fito a matsayin babban ɗan takarar adawa ga Janar ɗin, an harbe shi a wani hari da sojoji suka kai a ranar 28 ga Fabrairu, a cewar jam'iyyarsa.

Halartar manyan shugabannin ƙasashen duniya zuwa bikin rantsawar zai nuna irin karɓuwa da kuma goyon bayan da shugaban mai shekaru 40 ya samu.

Matsayin Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda ya je birnin N'Djamena a shekarar 2021 domin yin mubaya'a ga marigayi Marshal Deby kafin ɗansa kuma magajinsa ya hau kan mulki, ya tura ministan harkokin waje da kasuwanci na Faransa, Franck Riester domin ya wakilce shi.

Kasar Chadi na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya, kana ita ce ƙasa ta ƙarshen a yankin Sahel da Faransa ke jibge da sojojinta 1,000, kuma Macron na ɗaya daga cikin shugabannin da suka taya Deby murnar lashe zaɓensa.

Ƙasashen yankin Sahel da dama da ke fama da tashe-tashen hankula sun ƙarfafa alaƙa da Rasha bayan yanke hulɗarsu da birnin Paris.

Shugaban Rasha Vladimir Putin na cikin waɗanda suka fara taya Deby murna, sannan irin tawagar da Moscow ta aika zuwa birnin N'Djamena domin halartar bikin, ta yi matuƙar ɗaukar hankali.

AFP