Shugaba Erdogan ya samu kuri'u masu dumbin yawa wanda kiris ya rage ya ci zabe a zagayen farko. Hoto/AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a ranar Lahadi ya sake jaddada wa wadanda suke ganin abu ba zai yiwu ba kan cewa bai kamata su rinka yin riga malam masallaci ba musamman idan aka zo wurin bai wa jama’a dama su zabi shugaban da suke so.

Zaben da aka yi a Turkiyya ya kasance Erdogan ne ke gaban Kemal Kilicdaroglu, dan takarar Jam’iyyar CHP mai kawancen jam’iyyu shida. An tafi zagaye na biyu a zaben shugaban kasa a daidai lokacin da Erdogan ya samu kashi 49.51, inda ya rage saura kiris ya samu kashi 50 da yake nema domin ya yi nasara.

A majalisa ma, jam’iyyar Erdogan wato AK Party da kawayenta wato MHP da kuma Yeniden Refah sun samu kaso mai yawa. Erdogan da kuma AK Party sun samu nasara a zabuka da dama tun bayan da suka hau kan mulki a 2022.

Amma duk wanda ya zo kan taken labari irin wannan – ‘E, mulkin Erdogan zai iya karewa a karshen wannan makon’ – a wata jarida wadda aka wallafa a wata kasa zai iya tafiya da tunanin cewa babu makawa ‘yan adawa za su yi nasara.

“Akwai kafafen watsa labarai na kasashen yamma da dama da dagangan suka rinka nuna bangaren adawa a matsayin wanda zai ci zabe saboda yadda shugaban Turkiyya ke da kwarjini da kuma samun nasara da kuma soyayyar da ake nuna masa,” in ji Klau Jurgens, wani mai sharhi kan siyasa da ke zaune a Istanbul.

“Wadannan duk wasu shikashikai ne da shugabanninsu ba su da su a halin yanzu,” kamar yadda ya shaida wa TRT.

An kammala kidaya kuri’un zaben shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisa, inda kuma hukumar zaben Turkiyya YSK ta sanar da cewa za a je zagaye na biyu a ranar 28 ga watan Mayu a zaben shugaban kasa tsakanin shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan da kuma shugaban bangaren adawa Kemal Kilicdaroglu.

Ko ma dai mene ne, adadin da aka samu na kashi 89 cikin 100 na wadanda suka fito zabe ya sake tabbatar da yadda Turkiyya take a kasar Dimokradiyya.

An gudanar da zabe lami-lafiya ba tare da rahoton wata tarzoma ba a kasar. Akalla mutum miliyan 64.1 suka jefa kuri’a.

Gabannin zaben kasar, akwai masu sharhi da kuma kuri’un jin ra’ayi da suka yi hasashen cewa karshen gwamnatin Erdogan ya zo.

Me ya sa kafafen watsa labaran kasashen yamma suka yi kuskure

A lokacin yakin neman zabe, Erdogan da kuma Jam’iyyar AK Party sun yi kokarin fito da irin nasarorin da suka samu – tun daga kan samar da ababen more rayuwa na zamani zuwa kuma kaddamar da makamai na zamani – wadanda za su sa ‘yan Turkiyya su yi alfahari da kasarsu.

An rinka saka hotunan irin ayyukan da Shugaba Erdogan ya yi a sansanonin yakin neman zaben Jam’iyyar AK: jirgi mara matuki na TCG Anadolu da motocin lantarki na Togg.

“Turkiyya ta kara karfi, ana girmamata a yankin Turai da kuma duniya, ba karamar kasa ba ce tun da ba ta yin abin da kasashen duniya suke tilastawa a yi. Kafafen watsa labarai na kasashen yamma suna kuskure dagangan,” in ji Jurgens.

Erdogan, wanda Musulmi ne, ya kammala yakin neman zabensa a babban Masallacin Ayasofya, da karatun Al-kur’ani. Ayasofya (Hagia Sophia), an mayar da shi masallaci a 2020, shekara 80 bayan da aka mayar da shi wurin tarihi.

Matakin, wanda Kotun Kolin Turkiyya ta dauka, akwai kasashen yamma da dama wadanda suka caccake shi.

“Erdogan ba ya durkusa wa kasashen yamma,” in ji Yasser Louati, wani mai sharhi na kasar Faransa.

“Kasashen yamma suna son gwamnatoci masu musu biyayya. Suna son su ga shugabannin kasashen waje suna bin ra’ayinsu da manufofinsu.”

Misali, Faransa ba ta ji dadi a lokacin da Turkiyya ta cire haramcin da aka saka na mata da ke saka dankwali ba a makarantu da kuma jami’o’i a shekarun 2000, in ji shi.

A karskashin mulkin Erdogan, kasar ba ta daina harkokin diflomasiyyar da take yi a yankin ba.

Tun daga Syria zuwa Libya da gabashin Tekun Mediterranean, Turkiyya ta fito a matsayin kasar da take da tasiri.

Yadda Turkiyya ta yi adalci kan yakin Rasha da Ukraine, ya bai wa Brussels haushi, inda kasar take so Turkiyya ta saka takunkuman tattalin arziki masu tsauri a kan Rasha.

TRT World