A cikin kasar kuma, akwai akwatunan zabe kusan 192,000 da aka bude har zuwa karfe 5 na yammacin ranar zaben a kasar /Hoto: AA

Za a yi zabe zagaye na biyu a Turkiyya ranar 28 ga watan Mayu, bayan da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya samu kashi 49.5 na jumlular kuri'un da aka kada - inda ya rage masa kaso kalilan ya cike kashi 50.1 da ake bukata don samun nasara - yayin da abokin hamayyarsa Kemal Kilicdaroglu ya samu kashi 44.89 cikin 100 na jumullar kuri'un zaben da aka yi a ranar Lahadin da ta gabata.

Masu sharhi kan al'amuran siyasa na ganin wannan zagayen zabe da za a je a matsayin wata shaida ta yadda kasar ke tabbatar da tsarin dimokuradiyya.

Wata Farfesa a Sashen Nazarin Hulda da Kasashen Waje na Jami'ar Medeniyet da ke Istanbul, Dokta Ozden Zeynep Oktav, ta ce "Yawan mutanen da suka kada kuri'a a zabukan Turkiyya ya nuna yadda dimokuradiyya ke sake samun wajen zama sosai a kasar."

Jam'iyyu fiye da 30 da kuma 'yan takarar majalisar dokoki masu zaman kansu 150 ne suka fafata a zabukan da aka yi ranar Lahadin.

Omer Celik, mai magana da yawun Jam'iyyar AK, ya bayyana abin da gudanar da zabuka ke nufi ga Turkiyya, yana mai cewa "babban arzikin da kasar nan ke da shi shi ne yadda 'yan kasa ke da damar yanke hukunci kan zabar wanda zai mulki kasar tasu."

A jumlace mutum miliyan 64.1 aka yi wa rajista don kada kuri'a, inda kusan miliyan biyar daga ciki sababbin masu zabe ne, sai kuma miliyan 1.7 da suka yi zaben daga wasu kasashen waje da suke zaune.

A cikin kasar kuma, akwai akwatunan zabe kusan 192,000 da aka bude har zuwa karfe 5 na yammacin ranar zaben a kasar.

Jakadan Amurka a kasar Matthew Bryza, ya ce yawan mutanen da suka fita kada kuri'a (89%) a zabukan ranar Lahadin, babban ci gaba ne ga dimokuradiyya a Turkiyya, kuma yawan masu zabe irin wannan abu ne da Amurka za ta yi kishin samu a kasarta - inda kason masu fita zabe ba ya haura 65 cikin 100."

Kazalika Bryza, wanda tsohon jami'in Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ne a Fadar White House, ya jaddada cewa "yawan wadanda suka fita zaben alama ce da ke nuna yadda dimokuradiyya ke da muhimmanci ga Turkawa."

Wasu kuri'un jin ra'ayin jama'a sun yi hasashen cewa Kilicdaroglu ne zai ci zaben, lamarin da Bryza ya bayyana karara da cewa hasashen ba daidai ba ne, inda ya ba da misali da Zabukan Shugaban Kasar Amurka na 2020 da na 2016 da aka yi hasashensu ba daidai ba.

"Don haka ban yi mamaki ba kwata-kwata game da yadda [kuri’un jin ra’ayin jama’a] ba su yi daidai da ra’ayin jama’a ba game da zaben Turkiyya duk da cewa sun nuna cewa Kemal Kilicdaroglu yana gaban Shugaba Erdogan.

Ina ganin babu wani abu na makirci game da wannan – Ina ganin abu ne da ya sha faruwa a shekarun baya-bayan nan a kasashe ciki har da a Amurka yadda kuri’un jin ra’ayin jama’a ba sa yin daidai da abin da mutane ke so," in ji Bryza.

Sai dai Oktav ta ce "sakamakon zabukan sun nuna cewa kuri’un jin ra’ayin jama’a da kasashen waje suka gudanar da labaran kyamar Erdogan da kafafen watsa labaran waje suka yi ba su bayyana hakikanin gaskiyar lamari ba.

Sai dai wadannan irin kuri’u na jin ra’ayin jama’a da labaran sun nuna cewa Kiiıcdaroglu karen-farautar Amurka ne. Hakan ya rage kimar Kilicdaroglu a idanun Turkawa da dama."

A wani abu da watakila zai kasance karon farko na tafiya zagaye na biyu a zaben Turkiyya a sabon tsarin zabe, dukkan ‘yan takarar da za su fafata a zaben ranar 28 ga watan Mayu, Shugaba Erdogan da Kilicdaroglu sun bayyana kwarin gwiwarsu, kowannensu na amannar cewa zai yi nasara.

Bryza ya bayyana hakan a matsayin "wata alama ta karfin dimokuradiyyar Turkiyya cewa Kilicdaroglu da Erdogan kowanne ya yi amannar zai yi nasara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa.

"Kuma ina ganin hakan yana da kyau, yana da kyau sosai idan aka kwatanta da Amurka cewa shugaban kasa mai-ci Recep Tayyip Erdogan ya sha cewa zai amince da sakamakon zaben kuma yanzu mun ga yadda ya yi maraba da batun zuwa zagaye na biyu."

Bryza yana ganin hakan "ya sha bamban da abin da ke faruwa a Amurka yanzu, inda boren da aka yi ranar 6 ga watan Janairu a majalisar dokokin kasar ta Capitol Hill ya sanya alamar tambaya game da dorewar tsarin dimokuradiyyar Amurka kuma hakan abin kunya ne."

Bryza ya tuna yadda Shugaba Donald Trump "a makon jiya ya ki cewa zai amince da sakamakon zaben da za a yi a 2024 lokacin da dan jaridar gidan talbijin na CNN Kaitlan Collins ya tambaye shi ko zai yi hakan, sai ya ce zai amince da sakamakon zaben ne kawai idan sahihi ne."

Da yake bayani kan yadda Shugaba Donald Trump ya yi kuskuren yin ikirarin cewa an sace zaben 2020 kuma yake cewa zaben 2024 mai yiwuwa ya zama ba sahihi ba idan har ya fadi, to saboda an sace zaben ne.

Misalin da Shugaba Erdogan ya kafa abu ne mai kyau idan aka hada da misalin abin kunyar da Donald Trump ke fada,” in ji Bryza.

Oktave ta bayyana muhimmancin shekarar 2023 duba da yadda ta zo da gudanar da zabukan kasar da kuma tarihin samar da Turkiyyan.

"Zabukan 2023 na nufin abubuwa da dama ga Turkawa saboda a shekarar 2023 ne bikin cika shekara 100 na kafa jamhuriyar Turkiyya.

A hannu guda, mutane da dama sun yi amannar cewa Jam'iyyar AK za ta fadi zaben saboda ta shafe shekara 20 tana mulki, kuma tana shan suka sosai saboda hauhawar farashi da matsalolin tattalin arziki da take fama da su," in ji ta.

"Amma abin mamaki sai ga shi akasin hakan ya faru kuma Jam'iyyar AK ta samu rinjaye a majalisar dokoki.

TRT World