Hilda Baci: 'Yar Nijeriya na shirin kafa tarihin cin gasar Guiness World Records a fannin girki

Hilda Baci: 'Yar Nijeriya na shirin kafa tarihin cin gasar Guiness World Records a fannin girki

Ya zuwa ranar Litinin da karfe 08:32 na safe a agogon kasar, Hilda Baci ta shafe awanni 88 da minti 32 tana girki babu tsayawa.
Ana ta tattaunawa kan Hilda a shafukan sada zumunta. Hoto/Hilda Bassey

Wata matashiya ‘yar Nijeriya na shirin kafa tarihi na zama wadda ta fi daukar lokaci tana girki a duniya ba tare da tsayawa ba.

Ya zuwa ranar Litinin da karfe 08:32 a agogon kasar, Hilda Effiong Bassey, da aka fi sani da Hilda Baci, ta shafe awanni 88 da minti 32 tana girki.

Hakan na nufin Hilda, mai sana'ar girki a Jihar Legas da ke kudancin Nijeriya, ta doke takwararta ‘yar India Lata Tondon wadda ta shafe sa’o’i 87 da mintuna 45 tana girki a babu tsayawa a 2019 .

Matashiyar za ta ci gaba da girki domin ta tsawaita tarihin da ta kafa.

A wata hira da ta yi da ‘yan jarida, Hilda ta bayyana cewa tun tuni ta saka a ranta cewa za ta yi wannan girkin bayan da ta ga Lata ta yi.

Baci, mai shekara 27, ta soma wannan girkin ne a ranar 11 ga watan Mayu.

Batun nata ya mamaye shafukan sada zumunta musamman a Nijeriya da kuma Afirka inda aka yi ta karfafa mata gwiwa.

Cikin maudu’an da ake tattaunawa har da ‘Go Hilda’ a shafin Twitter.

Gwamnan Legas Baba Jide Sanwo-Olu ya yi takakkiya har wurin da take girkin a Legas inda ya ba ta kwarin gwiwa da kuma murnar cewa ana gudanar da wannan babban abu a cikin jiharsa.

Sanannun ‘yan Nijeriya da suka ba Hilda kwarin gwiwa

Cikin wadanda aka ga sun ba Hilda Bassey kwarin gwiwa har da zababben shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu inda ya tofa albarkiacin bakinsa a bidiyon kai tsaye wanda ake yi a Instagram na girkin.

Zabbaben shugaban kasar ya bayyana cewa yana ba ta gwarin gwiwa. Shi ma Atiku Abubakar wanda ya yi takarar shugaban kasa a 2023 a Jam’iyyar PDP ya nuna jin dadinsa dangane da aikin girkin da take yi.

Ya bayyana cewa ba abu bane mai sauki amma suna da yakinin a kanta kan abin da ta sa a gaba. Haka kuma ya bayyana cewa za ta kasance allon kwaikwayo ga miliyoyi sakamakon irin jajircewar da ta nuna.

We see you, Chef Hilda, standing at the crossroads of history, ready to carve your name in the annals of world records....

Posted by Atiku Abubakar on Sunday, May 14, 2023

Shi ma dan takarar shugabancin Nijeriya a Jam’iyyar Labour Peter Obi ba a bar shi a baya ba inda ya ce irin yunkurin da Hilda ke yi domin kafa tarihi ya fito da kokari da jajircewar ‘yan Nijeriya.

Ya kuma bayyana cewa yana mata fatan alkhairi.

Burna Boy wanda mawakin Nijeriya ne kuma wanda ya yi fice a duniya, ya taya Hilda murna tare da mata fatan alkhairi.

Soyayyar ‘yan Nijeriya ga Hilda

A yayin da ya rage sauran sa’o’i Hilda ta kai labari, wasu ‘yan Nijeriya da dama suka yi kaka-gida a gaban wurin da take girkin da ke Amore Gardens a Unguwar Lekki.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter ya nuna yadda jama’a suke tsaye ruwan sama na dukansu amma ko gezau.

Mutanen suna ta kalamai na kwarin gwiwa ga Hilda domin ganin ta samu nasara.

Wace ce Hilda Effiong Bassey?

Hilda 'yar asalin jihar Akwa Ibom ce kuma shekarunta 27.

Hilda ta shahara a fagen girke-girke domin kuwa tana sana’ar girkin abinci da kuma harkar fina-finai.

Ta gudanar da shirye-shiryen na girki a a talabijin da suka hada da “Dine On A Budget” da kuma “In my kitchen”.

Haka kuma ta fito a cikin fina-finai kamar Dream Chaser da Flatmates da Mrs Robert.

TRT Afrika da abokan hulda