An shafe sama da wata guda ana rikici a Sudan. Hoto/Reuters

Hare-hare ta sama da kuma karar harba makaman atilari sun karu a Khartoum babban birnin Sudan, kamar yadda wani mazaunin birnin ya bayyana.

Hakan na faruwa ne a yunkurin da sojojin kasar suke yi na kare muhimman sansanoninsu daga hare-haren mayakan rundunar RSF wadda suka kwashe sama da wata daya suna rikici da ita.

Rikicin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da RSF ya jawo sabbin rikice-rikice a wasu sassan Sudan, musamman ma a yankin Darfur, sai dai an fi mayar da hankali a Khartoum.

Wannan rikicin ya jawo matsalolin jinkai wadanda ke barazana ga yankin, inda sama da mutum 700,000 suka rasa muhallansu a cikin Sudan, da kuma tilasta wa kusan mutum 200,000 gudu makwabtan kasashe.

“Lamarin ya kai makura. Mun bar gidajenmu domin zuwa gidan makwabtanmu a Khartoum, inda muka guje wa yaki, amma luguden wutar da ake yi yana binmu duk inda muka je,” in ji Ayman Hassan, wani mazaunin birnin, mai shekara 32, a hirar da aka yi da shi ranar Talata.

“Ba mu san me ‘yan kasa suka yi ba da za a far musu da yaki a tsakiyar birninsu.”

Karanta karin bayani: Jerin abubuwan da suka faru wata daya bayan soma yakin Sudan

Rikici ya kara kamari a Khartoum da kuma Geneina babban birnin Yammacin Darfur tun bayan da bangarorin biyu suka gudanar da wata tattaunawa wadda Saudiyya da Amurka suka jagoranta a makon da ya gabata.

Tattaunawar da aka yi ta samar da wasu bayanai kan bayar da damar kai kayan agaji da kuma kare farar hula, amma matakan da za a bi wurin samar da hanyoyin da kuma amincewa kan tsagaita wuta na cikin abubuwan da ake tattaunawa.

Rundunar sojin ta fi luguden wuta ne da jiragen sama da kuma harba bama-bamai, a lokuta kalilan ne kawai take yin arangama ko yaki a kasa, a kokarin da take yi na tura mayakan RSF wadanda suke a wasu wurare a Khartoum bayan soma rikicin a ranar 15 ga watan Afrilu.

RSF din ta kai hari kan muhimman sansanoni da ke arewacin Omdurman da kuma kudancin Khartoum a ranar Talata a wani yunkuri na hana sojojin kai manyan makamai da kuma jiragen yaki, kamar yadda mazauna birnin suka bayyana.

Sojojin Sudan na ta kokarin yanke hanyoyin da RSF ke samun kayayyaki daga wajen birnin, da kuma kokarin kwace iko da muhimman wurare da suka hada da filin jirgin sama da ke Khartoum da kuma matatar mai ta Al-Jaili da ke Bahri.

An soma yakin ne bayan sabanin ra’ayi da aka samu tsakanin sojojin Sudan da kuma RSF inda sojin Sudan din suka so su mayar da RSF din a karkashinsu, duk a yunkurin mayar da mulki a hannun gwamnatin dimokradiyya.

Shugaban sojin Sudan Janar Abdel Fattah al Burhan da kuma kwamandan RSF Mohamed Hamdan Daglo, wanda aka fi sani da Hemedti sun samu manyan mukamai a majalisar sojin kasar Sudan bayan juyin mulkin da aka yi a 2019 wanda aka hambarar da Omar al Bashir.

Sun gudanar da juyin mulki bayan shekara biyu a lokacin da wa’adin mika mulki ga farar hila ya karato, amma duka bangarorin sai suka soma tattara dakarunsu a yayin da ake kokarin mika mulki ga farar hula.

TRT World