| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
CBN ya soke lasisin ƙananan bankuna na Microfinance 46 saboda rashin cika ƙa’idoji
CBN ya ce wannan mataki zai taimaka wajen tsaftace tsarin microfinance a Nijeriya tare da ƙarfafa bankunan da ke aiki bisa ƙa’ida da ƙarfi.
CBN ya soke lasisin ƙananan bankuna na Microfinance 46 saboda rashin cika ƙa’idoji
Bankin Tsakiya na Najeriya / Others

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin aiki na ƙananan bankuna na microfinance 46 a fadin ƙasar, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Yuli, 2026.

A cikin wata sanarwa da CBN ya fitar, an bayyana cewa an dauki matakin ne bisa ikon da aka ba bankin a karkashin Sassan 12 da 13 na Dokar Bankuna da Sauran Hukumomin Kuɗi (BOFIA) ta shekarar 2020.

CBN ya ce an amince da soke lasisin ne daga Gwamnan bankin, Olayemi Cardoso, bayan bankunan sun kasa cika muhimman ka’idojin da ake bukata domin ci gaba da gudanar da aiki a matsayin cibiyoyin kuɗi da aka bai wa izini.

Babban Bankin ya bayyana cewa dalilan da suka haifar da wannan mataki sun haɗa da ƙarancin kadarori da ba sa iya biyan basussuka, rufe aiki ba tare da amincewar CBN ba, da kuma dakatar da harkokin kuɗi gaba ɗaya.

Sauran dalilai sun haɗa da rashin fara aiki cikin watanni 12 bayan samun lasisi, da kuma gaza kiyaye mafi ƙarancin jarin da ba ya lalacewa saboda asara.

CBN ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarinta na kare kwanciyar hankali a fannin kuɗi, kare masu ajiya, da tabbatar da bin ka’idoji daga duk cibiyoyin kuɗi da ke aiki a ƙasar.

Haka kuma bankin ya jaddada cewa zai ci gaba da ɗaukar matakan sa ido da doka domin tabbatar da ingantaccen tsarin kuɗi mai aminci da ƙarfafa amincewar jama’a ga tsarin banki a Nijeriya.

A jerin bankunan da abin ya shafa akwai Microfinance Bank daban-daban daga jihohi da birane ciki har da Lagos, Kano, Abuja, Abia, Ogun, Kaduna da sauransu, wadanda suka haɗa da Gold MFB, Creditville MFB, CASHA MFB, Supreme MFB, da Avanus MFB.

CBN ya ƙara da cewa wannan mataki zai taimaka wajen tsaftace tsarin microfinance a Nijeriya tare da ƙarfafa bankunan da ke aiki bisa ƙa’ida da ƙarfi.

Rumbun Labarai
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta kama wasu mutane da kudade da ake zargin kuɗin fansa ne
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum biyu kan zargin kashe Danshagamu a Kano
Nijeriya ta naɗa sabon kwamandan yaƙi da ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram
NEMA ta karɓi ’yan Nijeriya 180 da aka mayar da su gida daga Libya
Sojojin Nijeriya sun kama wasu da ake zargin masu kai wa ’yanta’adda kayayyaki ne a Jihar Yobe
FIFA ta tura tawaga zuwa Nijeriya don gano ko gwamnati ta tsoma baki a murabus ɗin shugabannin NFF
INEC za ta ƙaddamar da na’urar bibiyar shirye-shiryen zaɓe kai-tsaye
An  kashe mutum 12, an jikkata 2 a sabon harin da Boko Haram ta kai wani ƙauye a Adamawa ta Nijeriya
‘Yanbindiga sun kashe mutum 10, sun sace 40 a wani ƙauyen Sokoto
Gwamnatin Jihar Filato a Nijeriya ta rufe makarantu saboda ɓarkewar cutar mashaƙo
NDC ta yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa kan ba ta da ’yan takarar gwamna a jihohin Nijeriya 12
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 36 da aka sace a kasar, sun kuma halaka ’yanta’adda da dama
‘Yanbindiga sun kashe mutum biyar tare da jikkata uku a wasu ƙauyukan Sokoto
Shari'ar Tinubu a Amurka ta neman haƙƙi ce ba ta laifi ba ce— Fadar Shugaban ƙasa
Darakta Janar na DSS ya umarci jami'ansu da kar su kama kowa yayin da farar-hula suka samu sabani
Nijeriya ta musanta zargin goyon bayan yunƙurin 'juyin mulki' a Nijar
Hukumar DSS ta Nijeriya ta ƙwato bindigogi 676 da harsasai 332,000
INEC za ta yi zaɓen gwaji na Shugaban Ƙasa gabannin zaɓen 2027 na Nijeriya
Ɓarayin daji sun ƙaƙaba harajin naira miliyan 40 kan mazauna wani gari a Sokoto
An lalata makarantu fiye da 1000, an kashe malamai 2,295 a Arewa maso Gabashin Nijeriya - Hukumomi