Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ƙasar ta rage dogaro kan kuɗaɗen shigar da take samu daga ɓangaren man fetur, yayin da gwamnati ke ƙoƙarin bunƙasa wasu ɓangarorin tattalin arziki.
Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata, yayin bikin cika shekaru biyar da kafa Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC) inda ya samu wakilcin Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a wajen taron.
Shugaban ya ce gwamnati na ƙara bunƙasa ɓangaren noma da masana'antu da harkokin fasahar zamani da ƙirƙire-ƙirƙire domin rage dogaro da ɓangaren mai.
Ya kuma ce haɗin gwiwar jami'an tsaro da kamfanonin mai da yankunan da ake haƙo mai da hukumomin sa ido duk sun taimaka wajen daidaita hanyoyin samar da ɗanyen mai.

A cewar Tinubu, masu zuba jari da suka bar Nijeriya a baya saboda neman wasu kasuwanni sun fara dawowa, matakin da ya ce ya sanya Nijeriya a kan gaba a Afirka wajen jawo jarin harkokin mai a tsawon shekaru biyu a jere.
Tinubu ya ce duk da rage dogaro da kuɗaɗen mai da Nijeriya ta yi, har yanzu ɓangaren man fetur da iskar gas na taka muhimmiyar rawa wajen samar da makamashi, da samun kuɗaɗen ƙetare tare da jawo hannayen-jari daga ƙasashen waje.
Ya ce Nijeriya za ta yi amfani da albarkatun mai da iskar gas wajen bunƙasa tattalin arziki masu yawa, maimakon ci gaba da dogaro da ɗanyen mai.
Shugaban ya kuma bayyana cewa iskar gas za ta ba da gudunmawa mai yawa a makomar makamashin Nijeriya, yana mai cewa wannan lokaci ne na “shekarun iskar gas”.
Tinubu ya ce gwamnati za ta ci gaba da tabbatar da bin ƙa'idoji da ɗaukar matakan da suka dace a ɓangaren mai, ciki har da cika alƙawuran shirye-shiryen aiki, da bunƙasa kayayyakin cikin gida, da kare muhalli da kuma tallafa wa al'ummomin da ake haƙo mai.
A nasa ɓangaren, Ministan Ma'aikatar Albarkatun Man Fetur na ƙasa, Heineken Lokpobiri, ya ce NUPRC ta samu gagarumar nasara tun bayan kafa ta shekaru biyar da suka gabata.
Ya ce a halin da ake ciki, Nijeriya na samar da kusan ganga miliyan 1.7 na ɗanyen mai a kowace rana, tare da tanadin mai da ya haura ganga biliyan 37.
Sai dai ya ce kasar na buƙatar ƙarin jari, sabbin zagayen bayar da lasisin haƙo mai da kuma kara bincike domin cin moriyar irin albarkatun da man fetur take da su.
Shugaban Hukumar NUPRC, Sanata Magnus Abe, ya ce kafa hukumar ƙarƙashin dokar Petroleum Industry Act na daga cikin muhimman matakan da Nijeriya ta dauka wajen sake fasalin ɓangaren mai da iskar gas.




















