| Hausa
NIJERIYA
4 minti karatu
Ba na da-na-sanin taimaka wa waɗanda suka yi watsi da ni a yanzu— El-Rufai
El-Rufai ya ce waɗanda shi ya agaza wa suna da ‘yancin zaɓan abin da suke so a yanzu da yanayinsu ya sauya.
Ba na da-na-sanin taimaka wa waɗanda suka yi watsi da ni a yanzu— El-Rufai
Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna ta arewa maso yammacin Nijeriya / Facebook/Nasir Elrufai

Tsohon gwamnan jihar Kaduna a Nijeriya, Nasir Ahmad El-Rufai, wanda a yanzu yake zaman waƙafi ya ce shi ba ya da-na-sanin taimaka wa waɗanda suka yi watsi da shi a halin da yake ciki a yanzu.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta mai taken “Abokantakata da abin da ya biyo baya,” El-Rufai ya ce ya ji wasu na nuna damuwa game da shiru da wasu mutane suka yi waɗanda ya taɓa mara wa baya a fili ko kuma ya bai wa tallafi na ƙut-da-ƙut a baya.

Ya ce a tsawon rayuwarsa yana yanke shawarar yin mu’amala da mutane ne bisa tanadin addininsa na Musulunci da tarbiyar arewacin ƙasar da ya samu da kuma ɗabi’unsa na kansa da yanayin zuciyarsa.

“Tsawon shekaru na tsaya tsayin-daka ga mutane da harkoki da na yi imani da su, a wasu lokuta a cikin yanayi mai wuya da kuma asara mai yawa,” in ji shi.

Ya ce irin waɗannan matakan bai ɗauke su ba bisa neman yabo ko godiya ko sakayya, amma bisa yaƙinin da yake da shi cewa su ne abubuwan da suka dace ya aikata.

El-Rufai ya ce waɗanda ya agaza wa suna da ‘yancin yin abin da suke so a yanzu da yanayinsu ya sauya.

Masu AlakaTRT Afrika - Jami'an tsaro sun ƙwace fasfon Nasir El-Rufa'i bayan yunkurin kama shi ya ci tura a filin jirgi

Ya ce wasu za su iya magana don mara masa baya, yayin da wasu za su iya yin gum da bakunansu ko kuma nesanta kawunansu daga abotarsu ta baya.

“Dalilansu nasu ne, kuma ba na so na yanke musu hukunci kawai saboda martaninsu ya sha bamban da abin da sauran mutane ko ma ni kaina zan yi tsammani,” in ji shi.

Tsohon gwamnan ya ce mawuyacin yanayi zai iya bayyana asalin irin dangantakar da ke tsakaninsu, yana mai ƙarawa da cewa abubuwan da ya gani cikin watannin da suka gabata za su iya sawa ya sake tunani a kan wasu abokansa.

“Mawuyacin hali yana da wata hanya ta haskaka dangataka,” in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa abin da ya gano a lokacin wahalar zai iya sawa ya sake nazari kan wasu dangataka “cikin nutsuwa ba tare da da-na-sani ba,” a cewar El-Rufai.

Sai dai kuma ya jadda cewa irin wannan sake tunanin bai kamata a yi masa kallon yin Allah wadai ko kuma suka ba.

El-Rufai ya ce bai yi da-na-sani ba bisa goyon bayan wasu mutane ko kuma harkoki da ya yi imanin cewa su ya kamata a yi.

“Ba na jin haushin wanda ya zaɓi kada ya yi mini irin hakan,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ya gwammace ya ci gaba da bin ƙa’idojin da suka jagoranci ɗabi’unsa maimakon ya bari matakan wasu su sauya waɗannan ƙa’idojin.

A kan ko wane abin da ake wa kallon rashin adalci da rashin godiya ko kuma ji masa, El-Rufai ya ce ba ya neman ramuwar gayya ko kuma sakayya.

“Ƙarshen fayyace gaskiya na Allah maɗaukaki ne, kuma na bar wannan hukuncin a gare shi, a wannan duniyar da lahira,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa kowa zai zauna da abin da ya zaɓa yayin da tarihi zai yanke hukuncinsa.

“Abin da ya dame ni kawai shi ne na kasance cikin nutsuwa da zuciyata kuma sama da komai da Allah maɗaukaki,” in ji shi.

Hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa sun kama El-Rufai, wanda ya mulki jihar Kaduna daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Yana fuskantar tuhume-tuhume ciki har da halasta kuɗin haram da karkatar da kadarorin gwamnati da hukumar ICPC ta gabatar, da kuma wata shari’ar laifi ta intanet da hukumar DSS ta shigar game da iƙirarin da ya yi cewa an yi kutse a wayar mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Ya musanta aikata laifi kuma ya ce shari’ar na da nasaba ne da siyasa.