Wasu ’yanbindiga sun kai hari wani ƙauye a tsakiyar Nijeriya da sanyin safiyar Asabar, inda suka kashe mutane da dama, ciki har da yara, lamarin da ya haddasa wani mummunan harin ramuwar gayya kan wasu rugagen Fulani makiyaya da ke kusa.
Rahoton tsaro da kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani ya ce maharan sun shiga ƙauyen Luman Ba’are, da ke Ƙaramar Hukumar Borgu, da misalin ƙarfe 6:00 na safe, lokacin da mazauna yankin ke shirin gudanar da sallar asuba.
Rahoton ya ce an kashe mutum 11, ciki har da yara ’yan ƙasa da shekara biyar da maigarin ƙauyen. Wasu daga cikin waɗanda aka kashe sun rasa rayukansu ne a cikin masallacin ƙauyen, wanda al’ummar Kambari ke zaune a ciki.
Rahoton ya ƙara da cewa an kuma yi garkuwa da wasu mazauna ƙauyen tare da tafiya da su zuwa wuraren da ba a sani ba.
Maharan sun kuma kwashe shanu, tare da ƙona gidaje da dama, shaguna da babura.
Wani mazaunin yankin mai suna Aliyu Usman ya shaida wa AFP cewa an jefa gawar hakimin ƙauyen cikin wutar da ke ci.
Sai dai rundunar ’yansandan yankin ta tabbatar da harin, amma ta ce mutum biyar ne suka mutu.
Bayan harin, wasu ’yan sa-kai daga ƙauyen sun kai munanan hare-haren ramuwar gayya kan rugagen Fulani makiyaya da ke ƙauyukan Wawa da Gadi Oli da ke makwabtaka da su, kamar yadda wani ma’aikacin agaji ya shaida wa AFP.
Ma’aikacin agajin ya ce lokacin da sojojin da ke wani sansanin soja da ke kusa suka isa wurin, lokaci ya ƙure.
’Yan sa-kai sun zargi mazauna Fulani da sanin waɗanda suka kai harin, amma suka ƙi taimakawa wajen daƙile tashin hankalin.
Ƙungiyoyin ’yanbindigar a yankin sun shahara wajen yin garkuwa da mutane da satar shanu. Sau da yawa suna kai hare-hare kan al’ummomin karkara a arewa maso yamma da tsakiyar Nijeriya, inda suke farmakar ƙauyuka da sata a gidaje.
Jihar Neja, inda aka kai harin, ta fuskanci hare-hare da dama a cikin ’yan watannin nan, ciki har da sace mutane masu yawa.














