| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
Osimhen ne waraka kuma hanyar tsira ga Manchester United karkashin Pochettino
'Yanwasan gaban United, Matheus Cunha da Bryan Mbeumo ba su kai matsayin gwaninta irin wadda sabon kocin ke buƙata a shirinsa na ceto ƙungiyar ba.
Osimhen ne waraka kuma hanyar tsira ga Manchester United karkashin Pochettino
Victor Osimhen na ta kwantiragi da Galatasaray har zuwa shekarar 2029. / AFP (Wire)
 

Masu hasashe game da makamar da ta rage wa Manchester United, suna ganin babu wanda ya cancanci ta ɗauko don neman tsira illa tauraron ɗanwasan Nijeriya, Victor Osimhen, wanda ke buga wasa a Galatasaray ta Turkiyya.

A makon nan ne United ta yi sabon koci, Mauricio Pochettino ɗan asalin Argentina, wanda kuma a baya ya riƙe ƙungiyoyin gasar Firimiya kamar Tottenham, Chelsea, da Southampton.

Rahotanni daga Ingila na cewa sunan Victor Osimhen ya sake dawowa bakunan masu ruwa-da-tsaki a Old Trafford, kuma a wannan karo Osimhen ya nuna cewa ƙofarsa a buɗe take.

Mai shekaru 27, haziƙin ɗanwasan yana da kwantiragi da Galatasaray har zuwa Yunin 2029, kuma yana karɓar kusan fam miliyan £13 duk shekara. Wannan ne ya sa duk ƙungiyar da ke burin samun sa sai ta shirya da kyau.

Sai dai kuma rahotannin na cewa babu saɗarar da ta ba da sararin sakin Osimhen a kwantiraginsa da Galatasaray. Don haka fatan ya sauya sheƙa a kasuwar Janairu mai zuwa ba ta hannunsa.

Kenan dole sai United ta shirya dabarun tattaunawa don shawo kan babbar ƙungiyar da ke tashe a Turkiyya, kafin a sakar mata Osimhen, wanda ta yi wa farashin fam miliyan £80 zuwa £100.

Girmama Galatasaray

A halin yanzu dai sabon kocin Manchester United, Pochettino yana da zaɓin ‘yanwasan gaba kamar Benjamin Sesko da Joshua Zirkzee, duk da dai babu ɗaya cikin biyun nan da ya kafa kansa sosai a matsayin abin dogaro.

Su ma sauran ‘yanwasan gaba kamar Matheus Cunha da Bryan Mbeumo, ba su kai matsayin gwanintar da sabon kocin ke buƙata a shirinsa na ceto United ba.

Tun farkon zuwansa Galatasaray a matsayin aro daga Napoli a 2024, Osimhen ya ci ƙwallaye 37 a kakar farko cikin duka gasanni.

Bayan komawarsa ta dindindin a bara kuwa, ya ci ƙwallaye 22 a kakar, kamar yadda a kakar bana da aka fara ma tuni ya ci har ƙwallaye 10 zuwa yanzu. Hakan ya taimaka wa ƙungiyar ci gaba da riƙe kambun gasar Super Lig.

Amma wani hanzari ba gudu ba, Osimhen yana matuƙar girmama Galatasaray saboda taimakon da ta yi masa lokacin da yake fuskantar ƙalubale a Napoli, da kuma ɗimbin masoyan da yake da su a Turkiyya.

Ko ma mai zai faru, Manchester United tana neman komawa tudun mun tsira bayan fara kaka da sakamako mafi muni a tarihinta ƙarƙashin Michael Carrick, wanda ya bar ta a ƙasan teburin Firimiya, cikin jerin masu faɗowa.

A yanzu dai za a jira ganin kamun ludayin Mauricio Pochettino, wanda zai jagoranci wasansa na farko a ƙarshen makon nan, a karawa da Liverpool.