Maharan ɗauke da makamai sun kai hari kan wani wurin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma wani ƙauye a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya, inda suka kashe mutane 17, a cewar hukumomin yankin.
Hare-haren na baya-bayan nan sun ƙara jefa al’ummomin karkara a arewa maso yamma da tsakiyar Nijeriya cikin fargaba, inda ’yanbindiga ke kai hare-hare kan ƙauyuka, yin garkuwa da mazauna da kuma wawashe ko ƙona gidaje.
A ranar Litinin, wasu ’yanbindiga da dama da ke kan babura sun kutsa cikin wurin haƙar ma’adinai da ke wajen ƙauyen Bindin, a ƙaramar hukumar Maru ta Zamfara, inda suka harbe masu haƙar ma’adinan zinariya biyar har lahira.
Daga nan ne suka shiga ƙauyen, inda suka yi arangama da sojoji tare da kashe mutum 12, a cewar hukumomin.
Sha’awar zinare
Mai ba da shawara kan harkokin ƙauyen, Abdullahi Musa Mutunji, ya tabbatar da mutuwar mutanen, yana mai cewa harin ramuwar gayya ne bayan wasu masu haƙar ma’adinai sun kashe wani ɗan bindiga da ya yi musu barazana.
Lawan Wanzam ya shaida wa AFP cewa ɗansa na cikin masu haƙar ma’adinan da aka kashe a harin na ranar Litinin, wanda ya ce wani shugaban ƙungiyar ’yanbindiga na yankin ne ya shirya shi.
Ƙungiyoyin ’yanbindiga kan kai wa ma’aikatan haƙar zinare da ke aiki ba bisa ƙa’ida ba hare-hare akai-akai, inda suke neman iko da wuraren haƙar ma’adinan da kuma kaso daga cikin zinare da ake samu.



















