| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Arda Guler ya tsawaita kwantiraginsa da Real Madrid zuwa 2031
Sabunta kwantiragin da Arda Guler ya yi wata alama ce da ke nuna Real Madrid tana bin tsarin riƙe matasan ‘yanwasanta a matsayin kadara don gina gobe.
Arda Guler ya tsawaita kwantiraginsa da Real Madrid zuwa 2031
Arda Guler ya zo Real Madrid ne a Yulin 2023.

Real Madrid ta bai wa ɗanwasanta na tsakiya ɗan asalin Turkiyya, Arda Guler sabuwar kwantiragi da za ta kai shekarar 2031.

Matashin ɗanwasan mai shekaru 21 ya sabunta kwantiraginsa da a baya za ta ƙare a 2029, kuma wannan ne karo na farko da yake tsawaita zamansa a ƙungiyar tun zuwansa a 2023.

Guler yana kakarsa ta huɗu a Madrid kuma ya samu shiga a wajen sabon koci, Jose Mourinho, kasancewar ana saka shi cikin ‘yanwasa 11 da ke fara wasa a-kai-a-kai.

A kakar bara, an saka Guler a farkon wasa har sau 40 cikin duka gasannin da Real madrid ta buga, inda ya ci ƙwallo shida da tallafin ƙwallo 14, wanda shi ne tallafi mafi yawa a ƙungiyar.

Tun bayan ritayar gwarzon ɗanwasan tsakiya na Madrid, Toni Kroos, Arda Guler ya samu damar taka muhimmiyar rawa a tawagar.

A cewar koci Mourinho, "Duk da dai waɗanda suka jagorance shi [Arda Guler] a cigaban da ya samu sannu-sannu tun zuwansa, su ya fi dacewa su faɗi cigabansa, amma basirarsa a fili take."

Sabunta kwantiragin da Guler ya yi wata alama ce da ke nuna Real Madrid tana bin tsarin riƙe matasan ‘yanwasanta a matsayin kadara don gobe.

Sauran taurarin Madrid da suka tsawaita zamansu akwai Aurelien Tchouameni, Trent Alexander-Arnold, Carreras, da kuma Espe, waɗanda zamansu zai kai shekaru bakwai masu zuwa.

Akwai ma irinsu Vinicius Junior da Marc Cucurella, waɗanda kwantiraginsu za ta kai 2032, yayin da Ousmane Diomande zai kai har 2033.