An kashe babban ɗan adawa na Chadi yayin da ake cikin hargitsi a babban birnin ƙasar

An kashe babban ɗan adawa na Chadi yayin da ake cikin hargitsi a babban birnin ƙasar

Dillo shi ne babban ɗan adawa da shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya wanda ya kasance ɗan'uwansa, wato Mahamat Idriss Deby Itno.
Dillo shi ne babban ɗan adawa da shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya wanda ya kasance ɗan'uwansa, wato Mahamat Idriss Deby Itno. AFP / Issouf SANOGO

An kashe shugaban ƴan adawa na Chadi Yaya Dillo a ranar Laraba yayin wata musayar wuta da jami'an tsaro, kamar yadda babban mai shigar da ƙara Oumar Mahamat Kedelaye ya faɗa.

An ji ƙarar harbe-harbe a ranar Laraba a N'Djamena, babban birnin ƙasar a kusa da hedikwatar jam'iyyar adawa, a cewar wani ganau na Reuters, bayan da tun da fari aka kashe mutane da dama a wani hargitsin da ya faru a ofishin hukumar tsaron cikin gida ta ƙasar.

Hukumomi sun zargi masu fafutuka na jam'iyyar adawa ta Socialist Party Without Borders (PSF), wacce Dillo ke jagoranta da tayar da hargitsin.

Dillo shi ne babban ɗan adawa da shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya wanda ya kasance ɗan'uwansa, wato Mahamat Idriss Deby Itno.

An saka ranar 6 ga watan Mayu a matsayin wacce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, inda Devy da Dillo duka suka ayyana aniyarsu ta tsayawa takara.

TRT Afrika