Ƙasashen da ke gaba-gaba wajen samar da makamashi mara tsafta sun shirya domin ƙara adadinsa, duk da alƙawarin da suka sha ɗauka kan sauyin yanayi. / Hoto: Reuters      

Daga

Sylvia Chebet

A matsayin shi na wanda ke yin amfani da galibin lokacinsa yana ƙididdiga a kimiyyance kan bala'o'in da ke kawo wa ɗan'adam koma-baya, mai bincike kan sauyin yanayi, George Mwaniki ya saba da jin mummunan labari.

Amma rahoton Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP) na baya bayan nan mai tsaurin gaske ne, ko da a wajen gwarzon kare muhalli kamar shi kuwa.

Rahoton ya nuna cewa sarrafa makamashi mara tsafta zuwa shekara ta 2030, zai samar da fiye da ninkin adadin da ake buƙata na dakatar da ɗumamar yanayi daidai da wanda ƙasashen duniya suka amince da shi, na 1.5 a ma'aunin digiri salsiyos fiye da na zamanin kafin yawaitar masana'antu.

Wannan batu ne na yin baki-biyu," Mwaniki ya faɗa wa TRT Afrika.

"Ƙasashe suna da bayyanannun aniya sosai a cikin kundayensu na NDC (kundin himmmatuwa na ƙasa), amma idan aka zo batun tsarawa da Kasafi na ƙasa, aniyarsu ta nuna ko-in-kula kan rage makamashi mai gurɓata muhalli tana fitowa fili," ya ce, yana tabbatar da ra'ayin Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres.

Ƙasashen da tattalin arziƙinsu ya dogara da makamashi mara tsafta sun fi yin karan tsaye wa ƙa'idojin da aka shimfiɗa.

A jawabinsa da ya zo tare da rahoton, Guterres ya bayyana cewa Rahoton Samun Giɓi Wajen Sarrafawa na 2023, wani zargi ne da ke nuna sakaci wajen shawo kan ɗumamar yanayi.

Rahoton, mai take, "Ƙasa ko Sama? Ƙasashen da ke kan gaba wajen Samar da Makamashi Mara Tsafta sun shirya domin ƙara adadin makamashin duk da alƙawarin da suka sha ɗauka kan shawo kan ɗumamar yanayi", ya nuna cewa gwamnatoci sun shirya samar da ƙarin makamashi mara tsafta da kusan kashi 110 a 2030 fiye da adadin da zai dace da rage ɗumamar yanayin duniya.

Masana kimiyya sun yi gargaɗin cewa hakan ya wajaba domin a kaucewa tasirin sauyin yanayi, kamar ƙaruwar bala'o'in dangin zaftarewar ƙasa da girgizar ƙasa da ambaliya.

Alƙaluma masu tayar da hankali

Rahoton Samun Giɓi Wajen Sarrafawan, ya samar wa ƙasashen da ke kan gaba wajen sarrafa makamashi mara tsafta wani sabon tanadi mai faɗi.

Waɗannan su ne Austaraliya, da Brazil, da Canada da China, da Columbia, da Jamus, da Indiya da Birtaniya,da Indonesiya, da Kazakhstan, Kuwait, Mexico, Najeriya, Norway, Qatar, Russia, Saudi Arabia, Afrika ta Kudu, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, da Ireland ta Arewa da kuma Amurka.

Girman jerin ƙasashen ya nuna cewa yawancin gwamnatoci na ci gaba da samar da muhimman manufofi da tallafin kuɗaɗe wajen samar da makamashi mara tsafta.

"Akwai wani karin magana da ke cewa, 'kar ka faɗa mani abin da ka damu da shi, nuna mani'. Game da muhawara a kan sauyin yanayi, ina ganin mun ga haƙiƙanin abin da ƙasashe suka damu da shi, sannan rage gurɓatacciyar iska zaɓi ne kawai a maimakon wajibi," Mwaniki ya koka.

A shekarar 2022, kamfanin Samar da man fetur na Brazil mai suna Petrobras ya samu wurare 68 nesa da gaɓar tekun Amurka ta Kudu da ya keɓe domin gano mai. Neman sabbin wuraren haƙo mai ya ƙara adadin kuɗi, Dala biliyan $6.9, da Amurka ke kashewa kan bunƙasa harkar samar da mai.

Kusan a lokaci guda kuma, kamfanin mai da yake da mazauni a Algeriya, Sonatrach, ya bayyana ƙudurinsa na ƙara adadin abin da yake samarwa domin ya zama ɗaya daga cikin manyan kamfanonin mai na ƙasa guda biyar a duniya zuwa shekarar 2030.

Duka waɗannan kamfanonin, tare da wasu 33 da suka mayar da hankali kan mai da iskar gas, sun tura tawaga Masar don halartar babban taro kan sauyin yanayi na shekara shekara na bara, COP27, da hadafin hana duniya kawo ƙarshen amfani makamashi mara tsafta kamar mai da iskar gas.

Da yawa mai yiwuwa su kasance a babban taron, COP28 wanda UAE za ta karɓi baƙunta, inda aka naɗa Sarki Al-Jaber a matsayin shugaban taron.

Yarda da cewa rage adadin gurɓatacciyar iskar gas na da muhimmanci wajen ceto duniya, Al-Jaber ya ce, "Wannan shi ne tudun mun tsiranmu. Shi ne alƙiblarmu ɗaya tilo. Yana amincewa da martaba kimiyyar ce kawai."

Da sauran aiki a gaba

Gaskiya mai ɗaci ita ce gwamnatoci dayawa suna shirin ƙara adadin samar da makamashin kwal a duniya har zuwa shekarar 2030, yayin da samar da mai da iskar gas a faɗin duniya zai ci gaba da ƙaruwa zuwa aƙalla shekarar 2050.

"A wani ƙaulin, gwamnatoci suna ninka adadin makamashin mara tsafta da suke samarwa; abin da yake nufin damuwoyi guda biyu ga mutane da kuma ga duniya," babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Guterres ya yi kashedi.

Ƙaruwar kuɗin haƙar mai na zuwa duk da cewa gwamnatocin ƙasashe 151 sun ɗauki alƙawarin kawo ƙarshen fitar da gurɓatacciyar Iska.

"Ba za mu iya magance bala'o'in yanayi ba ba tare da magance abin da ke haddasa su ba: Dogaro da makamashi mara tsafta. Wajibi ne COP28 ya nuna cewa zamanin makamashi mara tsafta ya zo ƙarshe - cewa ƙarshensa babu makawa. Muna buƙatar nagartacciyar himma wajen ƙara adadin makamashi mai tsafta, kawar da makamashi mara tsafta da kuma bunƙasa wadatar makamashi yayin da kuma ake tabbatar da hanyar sauyin mai adalci da daidaito."

Al-Jaber ya amince da cewa kawar da makamashi mara tsafta babu makawa. "Yana da muhimmanci... Amma wannan dole ya zama wani ɓangare na wani cikakken shirin sauyin makamashi mai ƙunshe da adalci, da hanzari, da tsari,da daidaito da kuma sanin Yakamata," ya buƙata.

Amma makamashi mai tsafta har yanzu bai kai ko kusa ba da matakin da ake so ya kai na biyan buƙatar makamashin mutanen duniya da ke ƙaruwa. Masu masana'antu sun ce wajibi ne a ci gaba da samar da mai da iskar gas "har zuwa nan gaba", don a kauce wa afkuwar iftila'i.

Yawancin harkokin kasuwancinsu na biliyoyin dala sun shafi gano inda za a samu ɗanyen mai ne, da haƙowa da tacewa - tare da ƙaddamar da shirye shirye wani lokaci na tsawon gwamman shekaru. Hakan na nufin lokaci mai tsawo bayan masana kimiyya sun ce wajibi ne duniya ta dena amfani da makamashi mara tsafta.

A ɗaya hannun, zuba jarinsu a fannin makamashi mai tsafta kaɗan ne ko ma ba su da shi kwata kwata, idan aka yi la'akari da tanadin dokokin kare haƙƙin dan adam ƙarƙashin yarjejeniyar Paris.

Abin da ba zai yiwu ba ne?

Sauyin yanayi yana tasiri kan ƴancin rayuwa,da kiwon lafiya, da abinci, da ruwa, da al'ada da kuma tsaftataccen, lafiyayye kuma ɗorarren muhalli. Al'ummomi da ake nuna wa wariya da mutane ƴan asalin waje sun ɗanɗana kuɗarsu a wajen bala'o'in dangin ambaliya da girgizar ƙasa, waɗanda ake sa ran za su ƙara ƙamari idan aka samu ƙarin gurɓatscciyar iska daga ƙona ƙarin makamashi mara tsafta.

Duk da hujja ƙarara cewa makamashin da ake ƙonawa kamar makamashi kwal yana fitar da sinadarin Methane dayawa, gurɓatacciyar iska mai ƙarfin gaske, mene ne yiwuwar kamfanonin mai da iskar gas za su yi watsi da ɗimbin riba, su tsunduma cikin harkar samar da makamashi mai tsafta?

"Yana da muhimmanci a fara yarda da cewa duniya ba ta ɗauki hanyar cim ma Muradun yarjejeniyar birnin Paris ba," Mwaniki ya faɗa wa TRT Afrika.

"Ya kamata mu dinga shiryawa domin magance mummunan tasirin ɗumamar yanayi, idan aka duba cewa wannan ya zama mana jiki".

TRT Afrika