Kungiyoyin ba da agaji sun kwashe tsawon watanni suna gargadin cewa, sakamakon cikas ga ayyukan jinƙai da kuma ƙarancin kudade, yunwa ta afka wa Sudan./Hoto: AFP

Watanni 10 kenan da yaƙin da ya jefa ƙasar Sudan ga "kusan rugujewa", akasarin mutanen ƙasar na cikin yunwa, kamar yadda Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.

"A wannan lokacin, ƙasa da kashi biyar cikin 100 na 'yan Sudan ke iya samun cin abinci sau ɗaya a rana," kamar yadda daraktan hukumar WFP na Sudan, Eddie Rowe, ya shaida wa manema labarai ranar Laraba a Brussels.

Tun a watan Afrilun da ya gabata ne Sudan ke fama da yaƙi tsakanin rundunar sojin ƙasar da dakarun sa-kai na RSF, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da haifar da abin da MDD ta kira "rikicin gudun hijira mafi girma a duniya".

Kimanin mutum miliyan 10.7 ne yaƙin da ake fama da shi a yanzu da kuma rikice-rikicen da ya ɓarke a baya ya raba da muhallansu, a cewar MDD.

Mutum miliyan tara ne suka rasa matsugunansu a cikin Sudan, inda Rowe ya ce "mummunar ta'azzarar rikicin da tashe-tashen hankula, da dakatar da girbin amfanin gona da yawaitar gudun hijira na ci gaba da jefa miliyoyin mutane cikin wani bala'i na jinƙai."

A duk faɗin ƙasar Sudan, wadda hukumar ta WFP ta ce tuni ta fuskanci matsalar ƙarancin abinci a duniya kafin yaƙin, mutane miliyan 18 na fuskantar matsalar rashin abinci a yanzu haka.

Daga cikin waɗannan, Rowe ya ce "kusan miliyan biyar na gab da fuskantar bala'i" -- suna fama da ɗaya daga cikin mafi munin matakin gaggawa da WFP ke amfani da shi, na biyu bayan yunwa.

Matsalolin da ake cin karo da su wajen kai agaji

Ƙungiyoyin ba da agaji sun kwashe watanni suna gargaɗin cewa, sakamakon cikas ga ayyukan jinƙai da kuma ƙarancin kuɗade, lamarin yunwa ya afka wa Sudan.

Amma irin wannan cikas na isar da agaji suna hana iya tantance girman bala'in.

A cewar Michael Dunford, daraktan yankin gabashin Afirka na WFP, akwai babban batu a cikin "samuwar bayanan don tabbatar da cewa an cim ma matsayar da ake buƙata don ayyana fari ko a'a".

Yayin da WFP ke iya kai kashi 10 cikin 100 na kayan agaji ga masu buƙata, "akwai manyan sassan ƙasar da ba za mu iya shiga ba," Dunford ya shaida wa manema labarai.

Yankunan da suka fi albarka a Sudan sun taimaka wajen kawar da yunwa, idan ba don faɗan ya mamaye yankunan noma na ƙasar ba.

A cikin watan Disamban 2023, wani kutse da dakarun soji suka sake yi ya sa yaƙin ya kai har zuwa jihar Al Jazira da ke kudu da Khartoum babban birnin ƙasar, inda aka shirya samar da mafi yawan hatsin Sudan a kakar bana.

TRT World