Gwamna Abba Kabir ne ya bayyana mayar da Sarki Sanusi II kan karagar mulki ranar Alhamis Hoto: Others Hoto/Majeeda Studio

Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya Abba Kabir Yusuf ya mayar da Muhammadu Sanusi II sarautar Kano.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi wa al'ummar Kano kai-tsaye ranar Alhamis, jim kadan bayan ya sa hannu kan gyaran dokar Masarautun Kano ta 2024 da majalisar dokokin jihar ta yi.

Gwamnan na Kano ya bayyana cewa hakan na nufin a yanzu a wannan jiha "Sarki ɗaya tilo muke da shi."

"Wannan yana nufin wannan Sarki shi zai ci gaba da riƙe ragama ta masarautarmu ta Kano baki ɗayanta," a cewar Gwamna Abba, a jawabin da aka watsa kai-tsaye ta kafofin watsa labarai da shafukan sada zumunta.

"Kowa ya riga ya san cewa bisa waccan doka ta baya wadda suka rusa suka lalata, Sarki Malam Muhammadu Sanusi Aminu Sanusi shi ne Sarki a wancan lokaci," in ji gwamnan na Kano.

Gwamnan ya ƙara da cewa "saboda haka bisa canji da aka yi na wannan doka, a yau ni ma na yarda, majalisa ta yarda, an dawo da Mai Martaba Malam Sanusi Lamiɗo Aminu Sanusi wannan kujera ta Sarkin Kano."

Da safiyar Alhamis ɗin nan ne Majalisar Dokokin Jihar ta Kano ta amince da gyaran dokar Masarautun Kano ta 2019, wacce ta yi sauye-sauye da dama kan masarautar Kano inda ta ƙirƙiri ƙarin masarautu huɗu masu daraja da ɗaya.

Gyaran dokar da majalisar ta yi a wannan makon ya soke duka sauye-sauyen da aka yi a baya, aka kuma koma amfani da tsohuwar dokar masarautu.

Sabuwar dokar ta 2024 ta fara aiki ne a ranar Alhamis bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sa mata hannu.

A lokacin da yake yi wa al'ummar Kano jawabi, gwamna Abba Kabir ya umarci sarakunan Kano biyar da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta naɗa da su fice daga gidajen sarauta, tare da miƙa duka kayan sarauta ga Kwamishinan Ƙananan Hukumomi na jihar.

"Ina so na yi kira ga sauran sarakuna, waɗanda wannan doka da aka cire ta shafa, cewar su yi ƙoƙari su bar gidan gwamnati cikin awa 48, su tabbatar da cewa sun bar gidan gwamnati, sun bar fadar Sarki da ofisoshinsa," kamar yadda ya faɗa.

Ya kuma umarci tuɓabbun sarakunan su gaggauta miƙa wa Mataimakin Gwamnnan Kano wanda shi ne Kwamishinan Ƙananan Hukumomin jihar takardun barin aiki.

A ranar 9 a watan Maris ɗin 2024 ne gwamnatin Kano ta Abdullahi Umar Ganduje ta sauke Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano saboda wasu dalilai da gwamnatin lokacin ta zargi shi da su.

Dalilan sun haɗa da zargin rashin biyayya ga gwamnati, da shiga siyasa, da zargin sukar manufofin gwamnati, da son 'kare martabar Kano', kamar yadda gwamnatin ta bayyana a lokacin.

Da wannan mataki dai, Sarki Muhammadu Sanusi ya zama Sarkin Kano na farko da aka sauke daga mulki aka kuma sake mayar da shi a cikin fiye da shekara 500, sannan Sarki na biyu da ya yi sarautar Kano sau biyu a tarihin sarautar Kano cikin fiye da shekara 1,000.

Gwamnatin Ganduje ta sauke Sanusi Lamido Sanusi ne bayan ya yi shekara biyar da wata shida yana sarauta.

A ranar 8 ga watan Yunin 2014 gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso ya naɗa Muhammadu Sanusi Sarkin Kano na 14 a jerin Sarakunan Fulani, bayan rasuwar marigayi Sarki Ado Bayero.

Wasu bayanai da suke fitowa daga mutanen da ke kusa da Sarkin, suna cewa ana sa rai zai isa birnin Kano ranar Juma'a.

A ranar Alhamis ya halarci wani taro kan tattalin arziki da aka gudanar a jihar Rivers da ke kudancin ƙasar.

TRT Afrika