Guguwar ta tilastawa iyalai da dama kwana a waje inda ruwan samake dukan su saboda rashin mafaka / Hoto: Cameroon News Agency / Photo: AP

A kalla gidaje 74 ne suka rushe sakamokon wata mahaukaciyar guguwa da ta faru garin Mbangasina da Ntui dake karamar hukumar Mbam da kim dake yankin tsakiyar Kamaru

Guguwar ta tilasta wa iyalai da dama kwana a waje tare da kayayyakinsu inda ruwan sama ke dukan su saboda rashin wajen fakewa, a cewar wani kamfanin dillancin labarai mai zaman kansa na Cameroon News Agency.

Sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Litinin ta ce shugaban karamar hukumar yankin Bernard Mboene ya bayyana irin barnar da guguwar ta yi wajen sanya mutane da dama rasa matsuguninsu.

‘’Abin takaici ne yanayin da mutanen nan suka tsinci kansu a 'yan kwanakin nan, zuwa yanzu dai mun kirga gidaje 74 da lamarin ya shafa tare mutum 358 ciki har da iyaye da yara da suka shiga cikin tashin hankali sakamokon rasa muhallansu’’ in ji Benard.

Mutanen da wannan iftila’i ya shafa sun shaida wa kamfanin dillacin labaran cewa ba su da tabbacin yaushe za su sake samun damar gina gidajensu da suka rushe saboda rashin kudi da suke fama da shi.

‘’A shekaru da dama ina zama da ni da iyalina a nan, kuma muna bin rayuwarmu a hankali. Yanzu kuma da wannan abin da guguwar nan ta janyo ban san ta inda zan fara ba neman matsuguni ba domin ba ni da komai.''

''Muna sha wuya wajen samun abincin da za mu ci sau biyu a rana, yanzu kuma ga guguwar ta zo ta kara dagula mana lissafi'', in ji wani da iftila'in ya shafa.

Ya kara da cewa ''Game da batun matsalar kudi da muke fama da ita, muna mika kokon bararmu ga gwamnati da ta kawo mana dauki, domin ba san inda za mu je ba ko abin da za mu yi ba.’’

Ko a wani taro na tunawa da ranar yanayi na duniya da aka gudanar kwanan nan, hukumomin asusun kula da muhalli na duniya sun gargadi al’ummomi da su guji sare bishiyoyi domin yin hakan zai iya zama illa.

Sun kuma ba da shawara kan cewa ana dasa irin bishiyoyin da za su girma su kuma taimaka wajen kare muhalli daga mummunar iska.

TRT Afrika da abokan hulda