A makon da ya wuce ne rundunar sojin kasar ta sanar da daukar sabbin ma'aikata.  PHOTO \ FILE \ AFP

Matasa 37 ne suka mutu sakamakon turmutsitsin da ya ɓarke a cikin dare a yayin wani aikin daukar sojoji a wani filin wasa da ke Brazzaville, babban birnin Jamhuriyar Congo, a cewar jami'ai a ranar Talata.

A makon da ya gabata, rundunar sojin kasar da ke tsakiyar Afirka da aka fi sani da Congo-Brazzaville, ta sanar da daukar ma'aikata 1,500 masu shekaru tsakanin 18 zuwa 25.

Firaiminista Anatole Collinet Makosso ya ce mutum 37 ne suka mutu a cikin "mummunan iftila'in," tare da jikkata wasu da ba a tantance adadinsu ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an kafa wani sashe don bincike a kan lamarin, a ƙarƙashin ikon Firaiminista.

An umurci masu neman aikin da su je wajen tantancewa a filin wasa na Michel d'Ornano da ke tsakiyar birnin Brazzaville.

A cewar mazauna yankin, akwai mutane da dama a cikin filin wasan a daren ranar Litinin lokacin da aka fara turereniya.

Wasu mutanen sun yi yunkurin bi ta kofar gida, inda aka tattake mutane da dama a garin turmutsutsun, kamar yadda mazauna garin suka ce.

Har yanzu babu cikakkun bayanai kan abubuwan da suka faru, kuma kamfanin dillancin labarai na AFP ya kasa tantance bayanan da ya samu.

AFP