Bayan jirgin Joola ya kife ya kasance a saman ruwa tsawon sa'a 16 kafin ya nutse. Hoto: Others       

Daga Charles Mgbolu

Yayin da agogo ya nuna karfe 11 na daren ranar 26 ga Satumban 2022, wani farin jirgin ruwa mai dauke da fasinjoji 1,800 wanda ya bar gabar tekun Gambiya ya ci karo da mummunan guguwa a Tekun Atlantic.

Iska da ruwan sama sun doki jirgin ruwan, sannan wata mahaukaciyar igiyar ruwa ta lalata gefen jirgin, abin da ya sa fasinjojin fara kururuwa cikin matukar tsoro.

Sunan jirgin ruwan Joola wanda mallakin kasar Senegal ne wanda ya bar gabar ruwan Ziguinchor a yankin Casamance da ke kudancin kasar Senegal da misalin karfe 1:30 na rana inda ya fara tafiyar sa'a 17. Zai je babban birnin kasar Dakar, zai yada zango ne a Tsibirin Carabane.

Joola ya yi tafiya mai nisa a teku fiye da tsawon tafiyar da aka bukaci ya rika yi a takardar lasisinsa kuma ba zai iya kaucewa kalubalen da zai bijiro sanadin hakan ba.

Minti biyar bayan ya shiga tsakiyar guguwar, sai ta fara yin tasiri a kansa, inda ya fara jirkitawa zuwa bangare daya kuma ya fara tangal-tangal yayin da ya fara cin karo da igiyoyin ruwa.

Alkaluman hukuma sun ce mutum 1,863 suka mutu a ruwan, inda mutum 64 ne kawai suka tsira da ransu.

Wannan ne mummunan hadarin jirgin ruwa da aka taba gani a Senegal kuma shi ne hadari na uku mafi muni wanda ba na soji ba da aka taba gani a tarihin duniya, inda ya wuce na jirgin ruwan Titanic wanda mutum 1,500 suka mutu a shekarar 1912.

Abokai da dangin Wakhani sun rasa ransu sanadin hadarin. Hoto: Wakhani Sambou

"Ya kamata na kasance a cikin jirgin. Ya kamata na kasance tare da su, amma sai na tafi buga kwallo a birnin Dakar," in ji Wakhani Johnson Sambou, wanda dan jarida ne a Senegal kuma ya rasa abokai da danginsa da dama sanadin hadarin, ya yi magana da TRT Afrika gabanin cika shekara 21 da faruwar al'amarin.

Cikin dimbin yara 'yan makaranta da ruwa ya ci akwai wasu yara 'yan tawagar kwallon kafa da ke kan hanyarsu ta fafatawa a wata gasa.

"Yara da yawa sun mutu saboda lokacin aka koma sabon zangon karatu, wasu daga cikinsu za su je babban birnin kasar, Dakar, don fara sabon zangon karatu," in ji Wakhani.

"Na rasa wasu aminaina. Tana cikin jirgin ruwa ne a karo na farko tare da 'yar uwarta. Ba a gano gawarwakinsu ba."

Sakaci

Binciken da gwamnatin Senegal ta yi ya dora alhakin faruwar hadarin ne a kan kuskuren dan Adam da sakaci, amma ba a kama kowa da laifi ba tukuna.

Adadin fasinjojin ya nunka adadin da ya kamata jirgin ya dauka har sau hudu, inda wasu fasinjoji da yawa suke saman jirgin.

Saboda yawan mutanen da ke cikin jirgin, abu ne mai wuya matukin jirgin wanda shi ma ya rasu ya iya hana jirgin nutsewa.

Wasu da suka shaida al'amarin sun ce lokacin da jirgin ya tuntsura an rika jiyo ihu wasu fasinjoji masu neman agaji har sai bayan da ya nutse tsawon mita 20 wato kimanin sa'a 16 bayan faruwar al'amarin.

"Aikin ceton bai yi sauri ba a lokacin. Lokacin da masu aikin ceton suka kai ga jirgin ruwan, ba su da manyan kayan aiki don ceto mutane da dama cikin kankanin lokaci," in ji Ibrahim Gassama, wani dan jaridan Senegal wanda ya rika kawo rahoto sosai kan hadarin jirgin ruwan Joola.

Hadarin ya rutsa da mutane da dama

An gina gidan adana kayan tarihi don tunawa da wadanda hadarin ya rutsa da su a birnin Ziguinchor a kusa da wata hanya mai cike da hada-hada da kuma Kogin Casamance. 'Yan kwangila suna kokarin kammala aikin a cikin shekara daya.

Amma Gassama ya ce dangin mutanen da abin ya rutsa da su suna bukatar abin da ya fi gidan tarihi.

"Suna so a tsamo tarkacen jirgin daga cikin teku. Wannan ce hanya daya tilo da za ta kawo karshen tunanin al'amarin ga mutane da dama. Suna so a kai jirgin gidan tarihi, saboda za a martaba 'yan uwansu da suka rasu."

Gwamnati ta ce har yanzu ba ta kammala hakan ba saboda wasu kalubalen aiki.

"Akwai kuma damuwar da wasu 'yan Senegal suke nunawa cewa tsamo ragowar tarkacen jirgin zai sake fama tsohon ciwo ne kawai," in ji Wakhani.

Saboda haka, ko Senegal ta koyi darasi daga wannan mummunan bala'i? Gassama ba ya tunanin haka.

"Kwana guda bayan hadarin jirgin, mu a matsayinmu na 'yan Senegal muka ce abin ba zai sake faruwa ba, kuma ya kamata mu sake dabi'unmu amma duka wannan bai wuce tsawon mako daya ba. 'Yan Senegal sun dawo da yin dabi'un da suka saba," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Bala'o'in da ke shirin faruwa

Wannan magana ce da ta shafi 'yan ci-rani marasa takardu da ke ketarawa Tekun Atlantic wadanda suke dandazo a Senegal wacce take yankin Afirka ta Yamma.

Kamar jirgin Joola, yawancin matasa 'yan Senegal suna ci gaba da mutuwa bayan sun kama hanya a cikin jiragen ruwa wadanda a lokuta da dama suke nutsewa bayan sun bar kasar Senegal yayin da suka hadu da guguwa.

Daruruwan 'yan ci-rani 'yan Senegal sun mutu a ruwa yayin da suke tafiya a jiragen ruwan da aka cika fiye da kima. Hoto: Reuters

Hadarin jirgin ruwa na baya-bayan nan shi ne wanda ya faru a watan Agustan bana inda fiye da 'yan ci-rani 'yan Senegal suka mutu a ruwa a gabar Tekun Cape Verde a kokarinsu na shiga Turai, kamar yadda Kungiyar Duniya kan Masu Yin Ci-rani (IOM) ta bayyana.

A kwanaki da watanni da suka biyo bayan hadarin Joola, akwai shirye-shiryen wayar da kan jama'a da yawa dangane da hadarin da ke tattare da cika jirgin ruwa da fasinja fiye da kima.

Gassama ya ce abin yana da daure kai yadda mutane ba sa amfani da hakan a rayuwarsu ta yau da kullum.

"A Senegal, ana cika jiragen kasa fiye da kima kuma akwai hadura a kan hanyar mota da yawa, inda mutane da yawa suke mutuwa saboda yadda ake take dokokin tuki. A matsayinmu na Senegal, ta yaya za mu manta da wannan?" in ji shi.

Dan uwansa dan jarida Wakhani shi ma yana da wannan ra'ayi. "Bai kamata mutane su yi wasa da rayuwa ba. Tafiya a teku ko titin mota ko ta jirgin sama duka suna tattare da hadari kuma wajibi mu rika bin dokoki."

Wakhani yana farin cikin cewa yawancin mutanen da suka tsira da danginsu sun ci gaba da rayuwarsu duk da zafin rashin da suka yi, ya ki tafiya.

"Zafin rashinsu ba za a iya mantawa da shi ba saboda mutuwarsu abu da za a iya kauce masa ba. Amma na yi amannar cewa dukkansu suna cikin aminci," in ji shi.

Yayin da ranar da hadarin ya faru ta zagayo, wadanda ala tilas suke rayuwa da tunanin yadda jirgin Joola ya nutse za su samu natsuwa, idan suka san cewa ba za a sake samun irin hadarin ba a nan gaba.

TRT Afrika