Karya darajar kudin Nijeriya ya janyo tashin farashin magungunan da ake shigo da su kasar daga waje: Hoto/Reuters

Daga Abdulwasiu Hassan

Musa Yusuf, mai sana'ar dinka kaya a Nijeriya, na neman yadda zai sayi maganin fitar haƙori ga 'yarsa 'yar watan takwas d ahaihuwa -- wanda ya tashi daga N7,000 ($7) zuwa N15,000 ($15).

Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Na yanke shawarar na nemi maganin gargajiya don magance ciwon hakorin da yarinyata ke fama da shi."

Hukumar Kula da Kayan Abinci da Magunguna ta Nijeriya (NAFDAC) a kwanakin nan ta yi gargadi ga mutane kan amfani da magungunan gargajiya da ba sa samun amincewarta a matsayin sauyi ga magungunan zamani, amma kuma tabbatar da hakan ya zama wani kalubale.

Farfesa Mojisola Adeyeye, darakta janar na hukumar ya ce jami'ansu na sanya idanu za su ci gaba da kai samame wuraren da ake sayar da irin wadannan magunguna na gargajiya.

Yusuf ya yi amanna da cewa maganin da ya sayarwa yarinyarsa na da amincewar NAFDAC, duk da cewa ba shi da tabbas kan hakan.

Mutane na zabar ko su sayi magunguna ko kuma su biya bukatunsu na dole saboda tashin farashin magunguna a kasar. Hoto/Reuters

To yaya batun ingancin maganin? "Zan iya cewa yana da inganci. Wannan maganin gargajiya ne da muka ga iyayenmu na amfani da shi," in ji mahaifin yara uku.

Tasirin kudi

Farashin magunguna a Nijeriya ya tashi sosai a baya-bayan nan sakamakon yadda kudin kasar, Naira ke rasa darajarta idan aka kwatanta da dalar Amurka.

Nairar da ake canja 463 a karbi dala daya, a yanzu ta kai sama da 1000.

Masu nazari na da ra'ayin cewa hakan na faruwa ne sakamakon tashin farashin magunguna a kasar da ke shigar da magunguna ko samar da magungunan da ake shigar da kayan hada su daga kasashen waje.

"Tun da dai mun dogara kan shigo da kayayyaki, sai ibtila'in karyewar kudinmu ya same mu. Ba a Nijeriya ake samar da mafi yawan magunguna ba," in ji Ahmad Danjuma, wani mai sana'ar sayar da magunguna da ya zanta da TRT Afirka.

"Yan watanni kadan da suka gabata, farashin magungunan ya tashi sosai. Idan ka sayi maganin 1,000 a Janairu, yanzu ya ƙaru sosai har ma ya ninka, saboda tasirin tashin farashi da na karyewar darajar kudin Naira."

Nijeriya ta dogara kan shigo da kayayyaki: Hoto/Reuters

Yusuf Hassan Wada, wanda ke da shagon sayar da magunguna, ya yi gargadi da cewa lamarin na iya lalacewa. A kokarin da suke yi na samun magani mai rahusa, wasu mutanen na fada wa hatsarin sayen jabun magani.

Wada ya shaida TRT Afirka cewa "A farkon shekarar nan, N4,000 ake sayar da 'Augmentin by GSK Pharmaceuticals'. A yanzu ana sayar da wannan magani tsakanin N20,000 da 25,000 a wasu kantinan."

"Wannan bambanci mai yawa na farashi na janyo mutane da dama su fada hatsarin amfanin da jabun magunguna ko marasa inganci wanda suna nan ana sayar da su sosai a kasuwanni."

Ba wai masu sayen magungunan ne kadai suke jin radadin tashin farashin kayayyaki ba.

Wada ya kuma ce "Tashin farashin cikin gaggawa na janyo babban kalubale ga sashen sarrafawa da sayar da magunguna. Kamfanunnuka da shaguna da dama sun rufe ko sun rage yawan kasuwancinsu."

"Rashin sayar da magungunan da kuma tsadarsu ya janyo ƙarancin ƙirƙirar kayayyaki a sashen kula da lafiya da kuma gaza sayo kayayyakin daga wasu wurare."

Ina mafita

Kamar yadda gwamnatin Nijeriya ta saka dokar ta ɓaci sakamakon tashin farashin kayan abinci, ƙwararru sun yi amanna da cewa ƙasar na buƙatar sauyin gaggawa don hana talakawa irin su Yusuf fuskantar tsananin tashin farashin magunguna.

Kudaden da 'yan Nijeriya da suke biya daga aljihunansu don kula da lafiya sun tura mutane da dama cikin talauci, kamar yadda wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya a kasar, Walter Kazadi Molumbo ya sanar.

"Ci gaba da yaduwa cikin sauri da cututtuka ke yi, tare da tsadar kula da lafiya, sun tsananta rayuwa. Karin 'yan Nijeriya da dama na fadawa cikin talauci saboda rashin lafiya sama d akoyaushe a 'yan shekarun nan," in ji Molumbo a wajen wani taro d aaka gudanar kwanan nan.

Wani kashi kadan na 'yan Nijeriya sama da mutum miliyan 200 ne suke amfana da tsarin inshorar lafiya na kasar.

Ƙwararru na da ra'ayin cewa karin mutane na bukatar su shiga karkashin tsarin inshorar ta yadda ba za su sha wahalar tashin farasin magunguna da karyewar darajar kudin kasar ba.

Wada ya ce "Wannan na bukatar kasar ta assasa tare da aiwatar da tsarin inshorar lafiya da bai wa jama'a kariya, a bayar da fifiko ga bukatun marasa galihu da ke cikin jama'a."

Wasu kuma na ganin cewa akwai bukatar gwamnati ta taimakawa kamfanonin samar da magunguna ta yadda za iya samar da masu rahusa, wanda hakan zai amfane su tare da masu amfani da magungunan.

Wada ya kuma kara da cewa "Za a iya cimma hakan ta hanyar samar da waus kudaden tallafi ga kamfanunnukan samar da magunguna, da kuma zuba jari, wanda duk za su hana dala hawa, su kuma bunkasa tattalin arziki."

Har sai an samar da wannan mafita mai ɗorewa ne, masu sayen magunguna irin su Yusuf da iyalansu za su daina neman magungunan da ba na zamani ba su daina jefa rayuwarsu cikin hatsari.

TRT Afrika