Mafarauta na kashe dabbobi domin samun sassan jikinsu don su sayar wa masu magani. Hoto/Reuters

Daga Ferdinand Mbonihankuye

Amfani da sassan jikin dabbobin daji da sassaken bishiyoyi domin yin maganin gargajiya ba sabon lamari ba ne a Burundi, sai dai tasirin hakan kan namun daji da kuma bishiyoyin ya soma tasiri.

Burundi na daga cikin kasashen da aka fi amfani da magungunan gargajiya a duniya.

Kusan kashi 80 na jama’ar Afirka sun dogara ne kan amfani da maganin gargajiya kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta tabbatar.

“A kasashen da ake da bayanai sosai, kason mutane da ke amfani da maganin gargajiya ya soma ne daga kashi 90 cikin 100 a Burundi da Habasha.

Sai kuma kashi 80 a Burkina Faso da Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo da Afirka ta Kudu da kuma kashi 70 a Jamhuriyyar Benin da Cote d’Ivore da Ghana da Mali da Rwanda.

Sannan akwai kashi 60 cikin 100 a Tanzania da Uganda,” kamar yadda WHO ta bayyana.

Sai dai akwai damuwa a Burundi inda wasu jama’ar suke da dabi’ar farautar namun dawa da kuma sare bishiyoyin daji domin neman magani.

Ana samun maganin gargajiya daga tsirrai da sassan jikin dabbobi. Hoto/ TRT Afrika

Mafarautan suna kashe dabbobin ne domin daukar fatarsu da sassan jikinsu, wadanda masu hada magungunan gargajiya ke saye musamman a lardunan da ke kusa da daji.

Gushewar dabbobi

Ana sayar da sassan jikin dabbobin a bainar jama’a a kasuwa a kuma farashi mai tsada na magunguna a kasar.

Hukumomi a kasar suna kokawa kan cewa wasu daga cikin mafarautan suna cinna wa daji wuta inda suke lalata muhallan dabbobin, suke kuma kashe wasu daga cikin namun dajin da suka hada da damisa da mesa da rakumin dawa da kuraye da gwanki domin maganin gargajiya.

Wannan yana barazana ga namun dawa a kasar. Masu sayar da maganin gargajiya a Burundi na ganin sassan jikin wadannan dabbobin wadanda suke amfani da su wurin yin magunguna suna warkar da muggan cututtuka kuma suna har warkar da guba.

Sai dai har su mafarautan sun amince da cewa adadin su kansu dabbobin da kuma bishiyoyin wadanda ake amfani da su domin maganin gargajiya yana raguwa.

Ana matukar amfani da magungunan gargajiya a Burundi. Hoto/TRT Afrika

“Wasu daga cikin wadannan bishiyoyin da kuma dabbobin sun gushe daga dazukan Burundi,” kamar yadda wani mai sayar da magungunan gargajiya Ntakanan Irimana ya shaida wa TRT Afrika.

Aloys Ntakananirimana daga garin Muruta na lardin Kayanza ya bayyana cewa a wani lokacin suna tafiya can cikin daji har zuwa kan iyaka domin samun wasu daga cikin dabbobin da kuma bishiyoyin.

Tsakanin al’ada da gargajiya

“Akwai wasu daga cikin dabbobin da suna wahalar samu, wasu tsuntsayen kuma babu su ma a Burundi, musamman mikiya da jinjimi,” kamar yadda wani mai maganin gargajiya ya shaida wa TRT Afrika.

A Burundi, ana daukar farauta a matsayin al’ada haka kuma ‘yan kasar da dama ba su dauki farauta wani abu mai illa ba duk da cewa adadin dabbobin yana raguwa. “Muna kashe dabbobin da fatarsu take magani.

Muna tsinke ciyawar da take amfani a gare mu,” in ji wani mai maganin gargajiya da ke lardin Kayanza wanda ba ya so a fadi sunansa.

Duk da cewa akwai dokoki da suke kula da namun daji, da farauta da kuma bishiyoyin da ke cikin daji a Burundi, ba a cika amfani da su ba.

Abel Nteziryayo, wanda shi ne alhakin kula da dajin Kibira ya rataya a wuyansa, ya bayyana cewa “duka masu maganin gargajiya suna bukatar amincewar hukuma” kafin su shiga dajin Burundi.

Hukumomi sun ce suna iya kokarinsu wurin magance matsalar farauta ba bisa ka'ida ba. Hoto/ TRT Afrika.

Sai dai ya koka kan cewa akwai masu shiga dajin ba kan ka’ida ba sakamakon dajin yana da girma kuma ba lallai masu gadin dajin su iya ganinsu ba saboda girmansa.

Wannan lamarin na sa wadannan dabbobin na daji da kuma bishiyoyin su kasance cikin barazana sakamakon masu farautar.

Wasu daga cikin mafarautan na cinna wa wani sashe na dajin wuta a yunkurin kashe dabbobin, inda a wani lokaci dabbobin ke guduwa zuwa wani sashe na garuruwa masu makwaftaka wadanda a hakan ma ba su tsira ba.

Matakin hukumomi

Masana sun bayyana cewa dabbobin suna bukatar wuraren da ke da kariya domin su haihu haka kuma dabbobi suna bukatar a kula da su kuma a kare su domin hana gushewarsu.

Sai dai hukumomi sun kara kaimi wurin wayar da kai domin sanyaya gwiwar masu aikata wannan aiki.

Haka kuma sun dauki tsauraran matakai game da mafarauta masu kunnen kashi.

Misali, a watan Satumbar 2022, akalla mutum shida aka kama kan zarginsu da kashe wani gwaggon biri a kauyen Mpfunda wanda ke kusa da dajin na Kibiria da ke lardin Kayanza.

An kama wadanda ake zargin a yayin da suke karkasa naman dabbar da ba su jima da kashewa ba.

Wasu daga cikin sassan jikin dabbobi da ake amfani da su wurin maganin gargajiya sun hada da fata. Hoto/ TRT Afrika.

Shugaban hukumar da ke kula da dajin na Kibira, Abel Nteziryayo ya shaida wa TRT Afrika cewa mutanen sun saba dokokin muhalli sakamakon gwaggon birrai na daga cikin dabbobin da ke fuskantar barazanar karewa.

“Idan masu maganin gargajiya suna bukatar wasu daga cikin fatun dabbobi, akwai bukatar su nemi amincewa daga ma’aikatar da ke kula da muhalli”, in ji shi.

Duk da cewa hukumomi na kokari wurin tabbatar da dokokin muhalli, masana na cewa akwai bukatar nemo sabbin hanyoyi domin habaka dabbobin da ke cikin daji.

TRT Afrika