A ranar 29 ga Mayu, 2024, 'yan Afirka ta Kudu za su jefa kuri'a. Jam'iyyar da za ta samu rinjaye a majalisar dokoki ce za ta kafa gwamnati mai zuwa. / Hoto: AFP

Daga Sylvia Chebet

Samun damammaki da dama a dimokuraɗiyya ya zama kamar wani muhimmin abu, amma kuma na iya kai mutane zuwa ga yanayin da masana tattalin halayya ke kira "Yawaitar zaɓi".

Masu jefa kuri'a su miliyan 17.6 na Afirka ta Kudu na iya fuskantar irin wannan hali a lokacinda aka fita jefa kuri'a a ranar 29 ga Mayu don zaɓar sabuwar gwamnati da za ta ɗora kan gwamnatoci uku da suka biyo bayan zamanin mulkin tsiraru farar fata.

Hukumar Zaɓe ta Afirka ta Kudu ta yi wa jam'iyyu 1,743 rajista - adadi mai yawa da zai iya yi wa dimokuraɗiyya wahalar kula da su, musamman ma a ce wanne za ka zaɓa. Yanayin zai fi haka girmama da a ce ba a soke jam'yyu 800 ba da kuma ƙin amincewa da kusan ɗari saboda wasu dalilai.

"Dandalin ya cika sosai," in ji David Monyae, mataimakin farfesa kan nazarin kimiyyar siyasa a Jami'ar Johannesburg yayin tattauna wa da TRT Afrika.

Ya yi nuni da cewa jam'iyyun da aka kafa shekaru da dama kafin ƙarewar mulkin tsiraru farar fata a 1994 na gogayya da sababbin jam'iyyu, waɗanda wasunsu ba su fi shekara guda da kafuwa ba, amma a hakan suke so su yi tasiri a siyasa.

A yayin da wasu 'yan jam'yyu sababbi za su iya tsallake wa, mafi yawan su za su mutu "da zarar an gama zabe".

To ta yaya masu jefa kuri'a a Afirka ta Kudu za su tantance aya da tskuwa a lokacin da suka je gaban akwatin jefa ƙuri'a?

Afirka ta Kudu na da jam'yyu sama da 1,700 da aka yi wa rajista amma ANC mai mulki da na adawa na DA da EFF ne suka fi yin shuhura. Hoto: AP

"Manufofin jam'iyyun kusan duk iri ɗaya ne. Kawai dai salon aika saƙon ne ya bambanta," in ji Monyae.

"Batutuwan da aka yi ta ambata su ne: farfaɗo da tattalin arziki da murƙushe cin hanci da rashawa da warware matsalolin ilimi da lafiya da raba filaye da kuɗaɗen walwalar al'umma."

Kasancewar abin da yake bambance jam'iyyun ba shi da yawa, ƙwararru na cewa takarar za ta zama tsakanin jam'iyyun da suka fi shuhura.

Batun "kishin talaka ne ya fi shuhura a bakin 'yan siyasa," in ji Monyae. "Ana yawan kaɗe-kaɗe da sumbatar yara."

A yayin da ake gangamin yaɗa manufa a tituna kafin ranar zabe, masu ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a sun fi karkata ne ga manyan jam'yyu uku a Afirka ta Kudu.

Jam'iyyar ANC

Tun 1994 ANC ke mulki a Afirka ta Kudu. An kafa ta a 1912, ita ce jam'iyyar siyasa mafi daɗewa a kasar mai tuta launin bakan gizo.

"ANC ta samu damammaki kuma ta yi ayyuka sosai, amma akwai matsaloli da ita kanta jam'iyyar ta amince da akwai su, kamar rashin tabbatar da adalci wajen mallakar filaye, wanda shi ne babban jigon gwagwarmayar ƙwatar 'yanci," in ji Monyae.

Da take kawo manufofin kawar da rashin adalci da daidaito da yaƙi da talauci da haɓaka adalci a tsakanin al'umma, ANC ta samu gagarumin goyon baya a kusan dukkan sassan ƙasar a tsawon shekaru 30 da take mulki.

Amma a shekaru goman da suka gabata, abubuwan kunya na cin hanci da rashawa da suka shafi manyan shugabanni da hauhawar farashi da ƙaruwar rashin aikin yi sun dakushe farin jinin jam'iyyar mai mulki.

Monyae ya shaida wa TRT Afirka cewa "ANC ta kasance jigon gwagwarmayar kasa. A wajen kowanne dan ƙishin kasa, idan muka kalle ta a fagen ƙasa da ƙasa da daɗewa a kan mulki yana kasancewa tsakanin shekaru 30 zuwa 40."

Shugaba mai ci Syrill Ramaphosa na jam'iyya mai mulki ta ANC na neman wa'adi na biyu a kan mulki. Hoto: Reuters

Masu nazari na cewa jam'iyyar ANC na iya samun ƙasa da kashi 50 na kuri'un da za a jefa a karon farko a cikin shekara 30.

Monyae ya yi amanna da cewa a yayin da dangantakar ANC da gwagwarmayar kawo sauyi ke zama wani babban abu da zai kai ta kusa ga samun nasara, dole ne ta yi 'yan dabaru don ganin ta kai ga gaci.

Ya ce "Wasu na da ra'ayin cewa ko da ANC za ta samu kashi 47 ko 48 % na ƙuri'un da za a jefa, ya kamata 'yan adawa su hade kai wajen zama karkashin inuwa guda. Amma sai 'yan adawar a rarrabe suke, kamar yadda jam'iyyar mai mulki take."

Haka kuma, yiwuwar kafa jam'iyyar haɗaka bai samu karɓuwa ba a wajen 'yan ƙasa da yawa.

Ya kara da cewa "ɗan ƙawancen da muka gani a matakin larduna da ƙananan hukumomi, abubuwan sun munana sosai."

Jam'iyyar DA

Jam'iyyar DA ce babbar jam'iyyar adawa a Afirka ta Kudu. An kafa ta a 2000, tana rajin kawo dimokuradiyya mai 'yanci da aiki da dokokin ƙasa da tattalin arziki mai haɓaka, waɗanda dukkansu sun ja hankali a wasu yankunan birane.

"DA kamar ta fito daga tsatson jam'iyyar DP ta fararen fata ce," in ji Monyae "Ta iya lashe zaɓuka a yankunan fararen fata da ke jihar Western Cape, amma tana fama wajen ganin ta samu karɓuwa a ɓangaren baƙaƙen fata."

Manyan jagororin jam'iyyar EFF da Julius Malema ke jagoranta da ke da rajin kawo sauyi sun gudanar da taro.

Jam'iyyar EFF

EFF ta fito ne daga tsatson ANC wadda aka samar a 2013 ƙarƙashin jagorancin shugaban matasan ANC Julius Malema.

Jam'iyyar na rajin kawo sauye-sauye a kowanne fanni musamman ma na tattalin arzikin Afirka ta Kudu da ya haɗka da mayar da dukkan masana'tu mallakar gwamnati da ƙwace filaye ba tare da biyan diyya ba.

"Duk da cewa wani ɓangaren adawa ce, ba ta da bambanci da ANC," in ji Monyae. "Mutum zai iya yi mata kallon nau'in ANC mai son kawo manyan sauye-sauye."

Baya ga matasa, jam'iyyar ta yi saurin samun farin jini a tsakanin waɗanda aka ɓata wa da suke kan tsarin siyasar gargajiya.

Monyae ya ce "Za ta iya zama kai da kai tsakaninta da DA ta fuskar goyon baya."

Jerin kalubale

Wasu ƙarin sanannu jam'iyyun Afirka ta Kudu su ne Inkatha Freedom Party (IFP) da Freedom Front Plus (FF+) da United Democratic Movement (UDM) da Pan Africanist Congress of Azania (PAC) da African Christian Democratic Party (ACDP) da kuma Socialist Revolutionary Workers Party (SRWP)

A yayin da ba su kai waɗancan ukun girma ba, masu nazari na cewa waɗannan jam'yyu na bayar da gudunmuwa wajen samun yanayin dimokuradiyya mai karsashi a ƙasar.

Manyan jagororin jam'iyyar EFF da Julius Malema ke jagoranta da ke da rajin kawo sauyi sun gudanar da taro.

Daga cikin sabbin zuwa har da jam'yyun Arise South Africa da Rise Mzansi da uMkhonto WeSizwe (MK), kuma za su iya yin tasiri.

MK, ita ma da ta ɓalle daga jam'iyya mai mulki, ta tsayar da tsohon Shugaban Ƙasa Jacob Zuma a matsayin ɗan takararta, amma a ranar 20 ga Mayu kotun kundin tsarin mulki ta Afirka ta Kudu ta yanke hukuncin cewa Zuma mai shekaru 82 ba zai iya tsaya wa takarar ɗan majalisa ba saboda an tuhume shi da cin hanci da zuwa kurkuku a 2021.

Monyae na da ra'ayin cewa wanzuwar Zuma ya zama kamar abun cutarwa ga ANC da kuma shugaba mai ci Syril Ramaphosa, sama da ƙalubalen kujerar shugaban ƙasar.

TRT Afrika