Shugaba Yoweri Museveni na yawan bayani game da yanayin cimaka da lafiyarsa. Hoto / Yoweri Museveni

Daga Susan Mwongeli

An wajabtawa ma'aikatan gwamnati a Uganda motsa jiki na awanni biyu a kowanne mako, a kokarin gwamnati na ganin sun samu cikakkiyar lafiya.

Shugabar ma'aikatan gwamnatin kasar ta Gabashin Afirka, Lucy Nakyobe, ta umarci dukkan shugabannin hukumomin gwamnati da su tabbatar da sun aiwatar da wannan umarni ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnatin Uganda ta kuma fitar da wani sako ta shafin X tana bayyana cewa an kirkiri wannan gangami ne "don magance cututtukan da ke damun su".

Wannan na zuwa makonni bayan mahukunta sun fitar da alkaluman yadda kiba ke daduwa a kasar daga kaso 17 zuwa 26 a shekaru 17 da suka gabata.

Shugabar ma'aikatan ta ce wannan matakin ya biyo bayan shawarar da ma'aikatar lafiya ta bayar, amma ba a fayyace ta yaya za a tabbatar da ana aiki da wannan ba.

Mayar da hankali sosai

A wasikar da ta aike, Nakyobe ta bukaci shugabannin hukumomin gwamnati da su mayar da hankali sosai kan wannna matu kuma su dauke shi da muhimmanci, tana mai cewa motsa jiki zai taimaka wajen kubutar da rayukan ma'aikatan gwamnati tare da rage wa gwamnati nauyin kula da lafiya.

Kwararrun kula da lafiya sun bayyana cewa rashin motsa jiki da cin abinci mara inganci na janyo kiba, wadda ke sanya hatsarin kamuwa da cututtukan zuciya, hawan jini, ciwon sukari da shanyewar barin jiki.

A shafukan sada zumunta na yanar gizo an yi maraba da wannan mataki inda ake bukatar gwamnati ta baiw ama'aikata karin hutun kwana guda don samun damar aiki umarnin.

"Tunani mai kyau, sai dai kuma zai fi kyau idan aka ce kowanne mai gida zia baiwa ma'aikacinsa hutun kwana guda don ya dinga motsa jini," in ji @RichieMafie

Wasu na tambayar ko an yi kasafin samar da wuraren motsa jiki ko bayar da kudi ga ma'aikata don su yi rejista.

A watan da ya gabata, Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce kashi 24 na mata da kashi 9 na maza a Uganda da ke da shekaru tsakanin 15 da 49 na fama da kiba.

"Yawaitar masu fama da cutar hawan jini da ciwon sukari a tsakanin matasa a Uganda na karuwa a hankali a cikin shekaru, inda mata ke da adadin da ya fi kowanne da kashi 27.7 da kuma 4.7 idan aka kwatanta da na maza da ya kama kashi 26.7 da 4.4," in ji WHO.

Hukumar ta ce ciwon zuciya, ciwon sukari da na numfashi na bayar da gudunmowar kaso 33 na mutuwar d aake yi a Uganda.

Ma'aikatar shari'a marar kiba

Ba wannan ne karo na farko da Uganda ta bukaci ma'aikatanta da su rage kiba ba.

A 2009, babban sakatare na lokacin a ma'aikatar shari'a Pius Bigirimana, ya kaddamar da motsa jiki na mako-mako tare da alkalai, majistare da sauran ma'aikatan ma'aikatar shari'a.

Shugaba Yoweri Museveni ya sha bayyana azamarsa ta motsa jiki da kuma raunin da Uganda ke da shi. A lokacin da cutar Covid-19 ta bulla, ya fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna shi yana mosata jiki, inda ya bukaci jama'a da su dinga motsawa sosai a loakcin da aka yi kulle.

A Rwanda da ke makotaka da Uganda, gwamnati ta kaddamar da ranar da ba za a fita da mota ba a Kigali a 2016, abin da mahukunta suka kira matakin yaki da cututtuka a rayuwa.

A wannan rana, masu babura da ke rwanda ma sun ajje nasu inda suka dinga amfani da kekuna ko tafiya a kafa. Lahadin farko, tsaki da karshen kowanne wata ce ranar da ba a fita da mota a Kigali.

TRT Afrika