Yadda fitattun mutane irin su Kevin Hart da Idris Elba suka halarci radin sunan jariran birai a Rwanda

Yadda fitattun mutane irin su Kevin Hart da Idris Elba suka halarci radin sunan jariran birai a Rwanda

An yi bikin radin sunan wanda ake yi duk shekara da ake kira Kwita Izina ne a ranar Juma'a a tsaunukan da ke Gandun Dajin Kinigi.
Wannan ne karo na 19 da Rwanda ke gayyatar fitattun mutane don rada wa jariran gwaggon birrai suna. Hoto: Kwita Izina

By Charles Mgbolu

An yi bikin radin sunan jariran gwaggon birai 23 a Rwanda.

An yi bikin radin sunan wanda ake yi duk shekara da ake kira Kwita Izina ne a ranar Juma'a a tsaunukan da ke Gandun Dajin Kinigi.

Fitattun mutane na duniya da suka hada da 'yan fim din Hollywood na Amurka Idris Elba da Kevin Hart, da mawakiya 'yar Nijeriya Asa, da 'yar fim 'yar asalin Zimbabwe da Amurka Danai Gurira ne suka halarci sunan jariran gwaggon birran.

Wannan ne karo na 19 da Rwanda ke gayyatar fitattun mutane don rada wa jariran gwaggon birrai suna a wani kokari na alkinta muhalli da ya hada da sanya al'ummomin yankin a ciki.

Bikin radin sunan na hekara-shekara kan samu halartar manyan mutane da masu fada a ji. PHOTO / TWITTER / RBA

Radin sunan ya samu halartar fitattun mutane sanye da kayan gargajiya na mafarauta a yayin da suke fadar sunan gwoggon birran daya bayan daya.

‘’Sunansa Gakondo,'' kamar yadda aka ji Kevin Hart ya ambata a wani bidiyo da aka nada aka kuma kunna a wajen taron.

Asa kuma ta rada wa wani birin suna 'Inganzo', wanda ta ce sunan yana da alaka da "tunawa da alkinta lafiya da duniyarmu."

Idris da matarsa Sabina Elba sun rada wa nasu birin suna ‘Narame', wato ‘rayuwa mai tsawo’.

Idris da Sabrina Elba sun halarci taron radin sunan. PHOTO / TWITTER / RBA

A cewar Kwamitin Ci gaba na Rwanda (RDB), fannin yawon bude-ido a bangaren gwaggon birrai na kasar shi ne ya fi jan hankali a kasar a 2022.

Shafin intanet na Gandun Dajin Virungu ya ce gwaggon birrai irin wadanda ake samu a kan tsaunuka, 900 ne kawai a dajin, kuma duk da kokarin da ake yi na alkinta su, suna fuskantar barazanar karewa sosai.

A kan kashe gwaggon birrai don a samu lambar yabo ko kuma don a ci namansu don samun martaba.

Bikin radin sunan na hekara-shekara kan samu halartar manyan mutane da suka hada da masu rajin kare muhalli da zakarun wasanni da shahararrun mutane da shugabanni da ma sauran al'umma.

TRT Afrika