Kenza Layli, mai faɗa a ji a shafukan sada zumunta kan salon rayuwa, ta yi nasarar ne a zazzafar gasar inda ta doke sama da 'yan takara 1,500 da suka fafata.

Wata ‘yar kasar Maroko mai sa hijabi da aka samar da ita da Ƙirƙirarriyar Basira ta yi nasarar lashe gasar kyau ta Miss AI ta farko a duniya.

Kenza Layli, mai faɗa a ji a shafukan sada zumunta kan salon rayuwa, ta yi nasarar ne a zazzafar gasar inda ta doke sama da 'yan takara 1,500 da suka fafata, lamarin da ya sa ta karɓi kambin da kuma babbar kyauta ta dala 20,000.

Kamfanin Fanvue World AI Creator Awards ne ya shirya gasar kuma an samu masu takara 10 a fafatawar ƙarshe.

"Duk da yake ba na jin farin ciki kamar yadda mutane ke ji, amma na yi murnar hakan," Layli ta faɗi hakan bayan lashe gasar.

Mata Musulmai a fannin fasaha

Wacce ta ƙera Layli, Meriam Bessa mai shekara 40 daga Casablaca, ta ce ta yi farin ciki.

"Wannan dama ce ta wakiltar Moroko cike da alfahari. Don haskaka matan Moroko da Larabawa da Afirka, da Musulmai a fagen fasaha,” kamar yadda Bessa, shugabar kamfanin Phoenix AI, ta shaida wa jaridar The Post a Amurka.

An yi bajekolin mutum-mutumi da dama na ƙirƙirarriyar basira masu mabambantan ɗabi'u a Gasar ta AI.

"Sha'awar duniya game da wannan lambar yabo ta farko daga [WAICAs] ta kasance abin ban mamaki. Kyautar wata hanya ce mai ban sha'awa don murnar nasarorin masu samar da AI da haɓaka matsayi, da tsara kyakkyawar makoma ga tattalin arzikin fasahar AI, "in ji daya daga cikin masu ruwa da tsaki a kamfanin Fanvue, Will Monange a cikin wata sanarwa da The Post ta wallafa.

Zazzafar fafatawa

Kenza Layli, wacce ke da mabiya 194,000 a Instagram, ta yi nasara a kan abokan fafatawarta irin su matan ƙirƙirarriyar basira na Faransa Lalina Valina da Olivia C daga Portugal.

Aitana Lopez, wata macen ƙirƙirarriyar basirar da aka tsara ta a matsayin ƙwararriya a fannin motsa jiki wacce ke cikin kwamitin alƙalan, ta yaba wa Layli bisa tsayin daka a gasar.

"Kenza yana da daidaiton fuska sosai kuma ta sami maki sosai a sassan jiki kamar hannu da idanu da tufafi," in ji Lopez.

"Burina ko yaushe shi ne in nuna alfahari da nuna al'adun Maroko tare da ba da ƙarin ƙima ga mabiyana ta fuskoki da yawa. Ina kuma alfahari da samun wannan lambar yabo ta Moroko," in ji Layli.

TRT Afrika